'Kudin Hayan Gida': Abin Da Yasa Na Yi Fallasa, Mataimakin Shugaban PDP Na Kasa

'Kudin Hayan Gida': Abin Da Yasa Na Yi Fallasa, Mataimakin Shugaban PDP Na Kasa

  • Ambasada Taofeek Arapaja, mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa ya yi karin haske kan dalilin da yasa ya yi fallasa
  • Arapaja tare da wasu jiga-jigan PDP uku da suka mayar da makuden miliyoyin da PDP ta tura musu sun ce ba su gamsu na halas bane
  • Arapaja, ya kuma musanta cewa bangaren Wike suke yi wa aiki, yana mai cewa su ba yara bane don haka babu wanda zai fada musu abin da za su yi

Mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Taofeek Arapaja, ya magantu kan dalilin da yasa shi da takwarorinsa a kwamitin ayyuka, NWC, na jam'iyyar suka mayar da kudi, yana mai cewa akwai wasu karin matsalolin kada yadda ake kashe kudaden jam'iyyar.

Arapaja, wanda ya musanta cewa yana yi wa bangaren Wike aiki ne, ya shaidawa Leadership Weekend cewa kudin da aka bayyana na sayar da fom bai yi dai-dai da adadin da jam'iyyar ta fada musu ba.

Kara karanta wannan

Ba Ta Bani Hakki Na: Miji Zai Saki Uwar 'Ya'yansa 8 Saboda Ta Daina Kwana Tare Dashi A Daki

Arapaja
Abin Da Yasa Na Yi Fallasa - Mataimakin Shugaban PDP Na Kasa. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba mu gamsu cewa kudin ya halast ba - Arapaja

Ya kara da cewa sun yanke shawarar mayar da kudaden ne domin sun gamsu cewa ba halas bane.

Arapaja, a hirar da ya yi da Leadership a karshen mako, ya musanta cewa mambobin NWC biyar da suka mayar da kudade zuwa asusun PDP bangaren Wike suke yi wa aiki, ya kara da cewa dukkansu ba yara bane kuma suna da hankalin da za su dauki mataki don kansu.

Ya ce:

"Wannan ba gaskiya bane. Mun fada maka dukkan abin da ya faru - kuma shine kawai. Mun yi imanin cewa kudin nan abin zargi ne. Me yasa ba a bamu ba sai yanzu. Muna da mutunci da ya kamata ku kare, wannan ba irin kudin da ya kamata mu karba bane."

Kara karanta wannan

Cin hanci: PDP ta yi martani, ta fadi dalilin da ya sa ta jika asusun bankin mambobin NWC miliyoyi

"Wasu abubuwan za su fito; mun ga N1 biliyan daya a nan, ani $2 biliyan a can. Abubuwa da dama suna fitowa. Ko kudin fom da aka sayar bai yi daidai da abin da aka fada gabatar mana ba.
"Ba mu gamsu kudin da aka tura mana ya halasta ba shi yasa muka mayar. Hakan baya nufin muna yi wa wani aiki. Mu ba yara bane."

Menene mataki na gaba?

Ya ce shawara ta rage wa Ayu ko ya yi murabus ko akasin hakan.

Kalamansa:

"Muna cikin mambobin NWC amma ba ni ne ciyaman ba. Shi kadai zai iya yanke shawarar ko zai yi murabus ko ba zai yi ba."

Shin za ku nemi a yi bincike na cikin gida?

Ya ce idan aka kai wurin za mu dauki matakin da ya dace.

"Idan muka isa gadar, za mu tsallake ta. NEC ce kadai za ta iya daukan wannan matakin."

Kara karanta wannan

Dawisun Namiji Mai Kyawawan Mata 8 Ya Ce Wasu Cikinsu Na Kishi Da Shi, Hotuna Sun Bayyana

A ranar Alhamis ne mambobin NWC biyar suka sanar da cewa sun mayar da Naira miliyan 151 da shugaban jam'iyyar na kasa ya biya su a matsayin kudin gida.

Yayinda Adagunodo, Orbih da Effah-Attoe suka mayar N28.8 million da kowannesu ya samu, Arapaja ya mayar da N36m.

Wadanda suka mayar da kudaden sune:

1. Mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa shiyyar kudu, Ambassador Taofeek Arapaja

2. Shugaban mata na kasa, Prof. Stella Effah-Attoe; mataimakin shugaban kasa na shiyar kudu maso kudu

3. Chief Dan Osi Orbih; mataimakin shugaban kasa na shiyar, Kudu maso Gabas

4. Dr. Alli Odefa; da mataimakin shugaban kasa na shiyar Kudu maso Yamma, Hon Olasoji Adagunobi-Oluwatukesi.

Tonon Sililin Wike: Shugabannin PDP 4 Sun Mayar Kudi N122m Da Aka Basu

Tunda farko, kun ji cewa akalla mambobin kwamitin gudanarwan jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party PDP hudu sun mayar da kudi N122.4 million baitul malin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Mayarwa Buhari Martani Bayan Ya Tsawatar Masa Kan Siyawa Jami'an Tsaron Jiharsa Makamai

A wasikun da suka aikewa jam'iyar, mambobin sun bayyana cewa an tura wadannan kudade asusun bankunansu ne ba tare da izini ko sanninsu ba, rahoton ChannelsTV.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164