2023: Tinubu Zai Ci Zabe Ko Ba Da Ku Ba, Tsohon Minista Ya Fada Wa Kungiyar Yarbawa Ta Afenifere
- Adebayo Shittu, tsohon ministan sadarwa na Najeriya ya ce ko da goyon bayan Afenifere ko babu, Tinubu zai ci zabe a 2023
- A cikin kwanakin nan ne shugaban riko na Afenifere, Ayo Adebanjo da wasu shugabanin yarbawa suka bayyana goyon bayansu ga Peter Obi na LP
- Shittu ya ce goyon bayan Adebanjo ba ta da tasiri duba da cewa cikin shekaru 23 da suka wuce bai taba cin zabe ba kuma tsufa ya fara rikita shi bai iya gane gaskiya abin da ke faruwa a kasa
Ogun - Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ya ce dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai ci zaben shekara mai zuwa ko da goyon bayan kungiyar Yarbawa da Afenifere ko akasin haka, Daily Trust ta rahoto.
Shugaban riko na kungiyar, Cif Ayo Adebanjo, da wasu shugabannin kungiyar sun goyi bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma, hakan ya raba kan wasu shugabannin yarbawa, wasu ke mamakin yadda kungiyar za ta mara wa Obi baya ta yi watsi da Tinubu wanda ake yi wa kalon 'na su'.
Martanin Shittu kan matakin na Afenifere
Da ya ke martani kan batun, Shittu ya ce goyon bayan da Afenifere ta bawa Obi 'ba barazana bane ga takarar shugaban kasa na Tinubu.'
Tsohon ministan, wanda shine jagoran kungiyar Tinubu/Shettima Coalition for good governance ya yi magana ne da yan jarida a Ota, Jihar Ogun, wurin taron siyasa da kungiyar 'Progressive Friends of Asiwaju Bola Ahmed Tinubu' ta shirya.
Ku kyalle Adebanjo, tsufa ce ta fara kama shi
Shittu ya yi kira da yarbawa su yi watsi da Adebanjo wanda ya ce bai san abin da ke faruwa a kasar ba kuma ba zai iya magana a madadin kabilar yarbawa ba.
Ya ce:
"Don me ra'ayin baba Adebanjo kan batun zai daga min hankali? A shekaru 22 da suka shude, baba Adebanjo bai taba cin ko kansila ba, ga kansa ko wadanda ya ke goyon baya.
"Don haka, wannan ba abin damuwa bane, gara in kawar da kai a maimakon cigaba da magana kan lamarin."
Ya cigaba da cewa:
"Baba Adebanjo bai taba goyon bayan Yarbawa ba kuma duk abin da ya ke yi ba shi da tasiri. Dukkan mu yarbawa ne, baba ya dara shekara 90 kuma ka san a irin wannan shekarar za ka masa izuri a siyasa da wasu abubuwan.
"Babu shakka Tinubu abin girmamawa da kauna ne a kasar Yarbawa, idan ba ma Najeriya ba. A kalla kashi uku cikin hudu na yan Najeriya na fatan Tinubu zai yantar da Najeriya, kuma zai sauya kasar, cewa zai zo ya dadawa talakawa da wadanda ake danne wa hakki."
Asali: Legit.ng