Yadda Na Ga Lafiyar Tinubu Kafin Ya Bar Najeriya, Ya Tafi Birtaniya Inji Jigon APC

Yadda Na Ga Lafiyar Tinubu Kafin Ya Bar Najeriya, Ya Tafi Birtaniya Inji Jigon APC

  • An samu wani babba a jam’iyyar APC da ya bayyana gaskiyar halin da Bola Tinubu yake ciki
  • Mutane suna yada labari mara tushe cewa ‘dan takaran shugaban kasar yana kwance babu lafiya
  • Wannan jigo a tafiyar APC ya fadi halin da ya samu Bola Tinubu ana daf da zai tafi kasar Ingilar

Abuja - Wani jagora a jam’iyyar APC mai rike da mulki a Najeriya, ya musanya rade-radin da ake ji na cewa ‘dan takaransu bai da lafiya.

Vanguard tace akwai masu yada jita-jita cewa Asiwaju Bola Tinubu bai da lafiya, yanzu haka yana jinya a wani asibiti da ke birin Landan.

Majiyar ta karyata wannan labari mara dadi da ya shiga kunnuwan wasu mutane a Najeriya.

Kamar yadda wannan jigo a tafiyar jam’iyyar APC ya shaidawa manema labarai, batun cewa Bola Tinubu yana ciwo, ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

"Na ga Tinubu ana awowai zai tafi"

A cewarsa, sai da ya hadu da ‘dan takaran a ranar Asabar, kafin ya wuce kasar Birtaniya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Asiwaju Bola Tinubu bai rashin lafiya. Na hadu da shi kafin ya tafi Landan a daren Asabar.”

- Majiya

Bola Tinubu
Sabon hoton Bola Tinubu a Landan Hoto: Ahmad Ganga
Asali: Facebook

Yawan jita-jita a kan lafiyar Tinubu

Masu yawo da wannan labari suna cewa tsohon gwamnan mai shekara 70 ya fara kwanciya a wani asibiti a Legas, kafin a fita da shi ketare.

Ba wannan ne karon farko da aka yada irin wannan labari, ana cewa ‘dan siyasar bai da lafiya ba, har yanzu babu wata hujja da ta nuna haka.

A jiya ne Ahmad Ganga wanda hadimi ne a majalisa ya wallafa wani sabon hoton Tinubu, yace an kashe bakin masu tambayar ina ya shiga.

Kara karanta wannan

Kamfen zaben 2023: Tinubu ya fadi sassan da zai tafi yawon kamfen a Najeriya

Tinubu v Wike

Jaridar ta tambayi ‘dan siyasar game da gaskiyar maganar haduwar mutanen Tinubu da kuma gwamnan jihar Ribas, Mista Nyesom Wike.

‘Dan siyasar ya bayyana cewa ko yau ‘dan takaran na APC ya sake samun irin wannan dama a Landan, za su kuma yin zama da Gwamnan.

Yayin da Tinubu yake Birtaniya, Nyesom Wike da takwaransa Samuel Ortom sun dawo Najeriya bayan sun yi ‘yan kwanaki a birnin na Landan.

Kwamitin kamfe zai karbi korafi

An ji labari Bola Tinubu mai neman takarar shugaban kasar Najeriya a 2023 a inuwar APC zai fadada kwamitin kamfensa mai mutum 422.

Ana tunani za a karo mutane 2000 da za su taya jam’iyyar APC yakin neman takara, majalisar kamfe za ta saurari Gwamnoni da APC NWC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng