Zan Jagoranci Najeriya Zuwa Ga Makoma Mai Kyau, Inji Dan Takarar APC Tinubu
- An yiwa 'yan Najeriya alkawura masu dadei, an lasa musu zuma a baki yayin da jam'iyyun siyasa suka fara gangamin kamfen gabanin zaben 2023
- Bola Ahmad Tinubu, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana kadan daga abubuwan da ya shirya yiwa 'yan Najeriya matukar suka bashi dama a 2023
- Tinubu ya ce ba shi kadai zai yi aikin ba, ya ce yana tare da abokin takararsa, kuma za su jajirce wajen kawo sauyi mai ma'ana ga ci gaban Najeriya
Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga abubuwan da ya shirya idan ya gaji Buhati bayan zaben 2023.
Ya matukar 'yan Najeriya suka zabe shi tare da abokin takarar sanata Kashim Shettima, to tabbas goben Najeriya za ta yi kyau ainun, Punch ta ruwaito.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a jiya Laraba 28 ga watan Satumba, inda ya kara da cewa, zai shiga lungu da sakon Najeriya domin tallata hajarsa ga kwadayin dalewa kujerar Buhari.
'Yan Najeriya su sa rai da ganin sauyi
Ya kuma bayyana cewa, yana fatan shi da Shettima su sake sanya fata a zukatan 'yan Najeriya, tare da yin abubuwan da za su kawo ci gaba ga kasar, rahoton jaridar Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da cewa, a yanzu duniya na fuskantar kalubale, don haka shi zai yi iyakar kokarinsa ya ga ya kawo sauyi mai amfanu ga 'yan Najeriya.
Don tabbatar da shirinsa, ya shaidawa duniya cewa:
"A shirye muke ni da abokin takara ta domin mu samar da shugabancin da zai habaka kasarmu, ya kuma daukaka martabarta ta hanyan sabon tunani, kirkirar sabbin dabaru da kuma hangen nisa."
Ban Sani Ba Ko Tinubu Yana Najeriya, Inji Jigon Kamfen Din Tinubu, Oshiomole
A wani labarin, mataimakin daraktan gangamin kamfen din APC, Adams Oshiomole ya ce bai da masaniya ko dan takarar shugaban kasansu na nan a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba 28 ga watan Satumba yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels.
Ya bayyana cewa:
"Ba da shi nake aiki kullum ba, ban san yana nan ko bai nan ba."
Asali: Legit.ng