Zan Yi Kamfen A ‘Kowane Sashe Na Najeriya’, inji Dan Takarar APC Tinubu

Zan Yi Kamfen A ‘Kowane Sashe Na Najeriya’, inji Dan Takarar APC Tinubu

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC ya bayyana cewa, zai taka kowane bangare na Najeriya domin tallata hajarsa
  • Ya fadi haka ne yayin da ake jita-jitar rashin lafiya ba za ta bari ya iya yawon kamfen ba a fadin kasar
  • A yau 28 ga watan Satumba ne aka buga gangar siyasa, jam'iyyun siyasa sun fara tallata 'yan takararsu a Najeriya

Najeriya - Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar APC, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana kadan daga shirinsa na kamfen din zaben 2023, Channels Tv ta ruwaito.

Tinubu ya ci alwashin cewa, zai taka kowane bangare a Najeriya domin tallata aniyarsa ta gaje kujerar Buhari a 2023.

A baya an yada jita-jitar cewa, akwai yiwuwar lafiyar Tinubu ta hana shi samun damar yawo a jihohin Najeriya da sunan kamfen.

Kara karanta wannan

Atiku Yace 'Yan Kabilar Ibo Zai Mikawa Mulki Idan Ya Kammala Wa'adinsa

Dan takarar APC ya ce zai taka kowane fanni na Najeriya a yawon kamfen
Zan Yi Kamfen A ‘Kowane Sashe Na Najeriya’, inji Dan Takarar APC Tinubu | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sai dai, wata sanarwar da ya fitar a yau Laraba 28 ga watan Satumba ta bayyana cewa, ya shirya tsaf domin yada sakonsa na aniyar gaje Buhari a fadin Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa:

"Yau ce ranar da aka fara gangamin kamfen takarar shugaban kasa na zaben 2023 a fadin kasar nan.
"Ina gayyatar dukkan 'yan Najeriya su hada kai da ni da sanata Kashim Shettima a wannan tafiya mai ban sha'awa kuma mai muhimmanci a shirinmu ya sake dawo da fatan jama'a a wannan kasa tamu Najeriya."

Daga nan ne Tinubu ya bayyana cewa, yanzu ne Najeriya za ta kafa tarihi, kuma bai kamata wani ya rasa wannan damar ba.

Hakazalika, ya ce ya kamata 'yan Najeriya su koyi darashi daga kura-kuransu na baya.

Ya kuma kara da cewa, a shirye yake daram, tare da abokin takararsa, za su ba da shuganacin da zai zama abin misali ga na baya.

Kara karanta wannan

2023: Matsaloli 5 da ke faruwa duk lokacin da aka fara kamfen a Najeriya

Majalissar Wakilai Ta Fusata Kan Rashin Karasa Aikin Titin Abuja Zuwa Kano Na N797bn

A wani labarin, majalisar wakilai ta Najeriya ta bukaci ministan ayyuka, Babatunde Fashola da ya gaggauta umartar kamfanin Julius Berger da ya koma bakin aikin kammala aikin titin Abuja-Kaduna-Kano, kuma ya fara daga titin Jere-Kaduna.

Wannan kira na majalisa na zuwa ne bayan da Garba Datti Muhammad da wasu 'yan majalisu 38 suka tado da batun a majalisa, Daily Trust ta ruwaito.

Idan baku manta ba, majalisr zartaswa ta kasa ta sauya kudaden da aikin zai ci a watan Maris din bara, inda ya koma N797.2bn daga N155bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.