Rikicin PDP: An Nemi Jonathan da Wasu Kusoshin Jam'iyya a Wurin Kaddamar da Litattafan Atiku
- Taron kaddamar da wasu litattafai na Atiku Abubakar da tawagar Kamfe ya ƙara tabbatar da rikicin jam'iyyar PDP
- Tsohon shugaba, Goodluck Jonathan, gwamna Wike da sauran yan tawagarsa ba su halarci wurin taron ba a Abuja
- Tun bayan kammala zaɓen fidda gwanin PDP a watan Mayu, abubuwa ke ta faruwa a jam'iyyar adawa
Abuja - Tsohon shugaban ƙasa, Dakta Goodluck Ebele Jonathan, bai halarci wurin taron kaddamar da Litattafai uku da rantsar da tawagar kamfe na ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar PDP ba.
Jaridar Tribune Online ta ruwaito cewa bayan Jonathan, mambobin kwamitin gudanarwa (NWC) na PDP masu goyon bayan tsagin Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas basu halarci wurin ba a Abuja.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa yanzu haka taron kaddamar da litattafan Atiku Abubakar da Tawagar Kamfe na gudana a dakin taro na ƙasa da ƙasa (ICC) dake birnin tarayya.
Ana ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin Atiku da tsagin gwamna Wike tun bayan ayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasan a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin PDP a watan Mayu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mafi yawan mambobin NWC na jam'iyyar PDP ta ƙasa sun shawarci Atiku ya zaɓi gwamna Wike a matsayin abokin takararsa, amma Wazirin Adamawa ya tsallake ya ɗakko gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa.
Tun wannan lokaci dai lamari ke ta ƙara dagule wa a babbar jam'iyyar hamayya, inda har ta kai ga 'yan tsagin Wike suka sanar da tsame hannu daga tawagar Kamfe.
Sunayen litattafan da Atiku ya ƙaddamar
Sunayen litattafan guda uku da Atiku ya kaddamar sune, "Tarihin Atiku Abubakar," da "Kes ɗin kundin tsarin mulki a Najeriya," da kuma "Sauya Fasalin ƙasa ne hanyar haɗa kai da samun cigaba."
Mahalarta taron guda biyu a wuri ɗaya
Daga cikin waɗanda aka hanga sun yi kane-kane da ɗakin taron akwai, gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, na Sakkwato, Aminu Tambuwa, na Taraba, Darous Ishaku, na Delta, Ifeanyi Okowa da Udom Emmanuel na Akwa Ibom.
Sauran sun haɗa da gwamna Douye Diri na Bayelsa, Godwin Obaseki na Edo, Ahmadu Fintiri na Adamawa, tsofaffin shugabannin majalisa, Bukola Saraki, Anyim Pius Anyim, David Mark da Ghali Na'abba.
Muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Ambasada Damagun, da tsohon shugaban jam'iyya na ƙasa, Uche Secondus, sun samu halartar wurin taron, jaridar Dailytrust ta ruwaito.
A wani labarin kuma Jerin Kasuwanci 6 da Zasu Amfana da Yaƙin Neman Zaben Shugaban Kasa 2023
A yau Laraba, 28 ga watan Satumba, 2022 jam'iyyu zasu kaɗa gangar yaƙin neman zaɓe domin tunkarar babban zaɓen 2023 kamar yadda hukumar INEC ta tsara a jadawalinta.
A lokaci irin wannan, akwai yuwuwar hada-hadar kuɗaɗe kan dalilai daban-daban. Alal misali lokacin zaɓen fidda gwanin manyan jam'iyyu, APC da PDP, ana ganin sun taka rawa wajen ƙarancin dalar Amurka a ƙasa.
Asali: Legit.ng