Tsohuwar Kwamishina a Ondo da Masgoya Bayanta 3,500 Sun Bar Jam’iyyar APC, Sun Koma PDP
- 'Yan siyasan Najeriya na ci gaba da duba inda ke da maiko domin tunkarar zaben 2023 mai zuwa nan kusa
- Tsohuwar kwamishina ta sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP, ta ja zugar wadanda ke mara mata baya
- PDP ta ci alwashin kwace mulki a hannun APC duk da rikicin cikin gida da jam'iyyar ke fuskanta a kwanan nan
Jihar Ondo - Shugabannin jam'iyyar PDP a yankin Kudu maso Yammacin kasar nan sun ce rikicin da jam'iyyarsu ke dama dashi ba zai hana su karbar mulki a hannun APC ba a zaben 2023.
Shugabannin sun fadi haka ne yayin da suke karbar tsohuwar kwamishinar ruwa na jihar Ondo, Yetunde Adeyanju da magoya bayanta 3,500 zuwa PDP a karamar hukumar Odigbo ta jihar.
Dubban magoya baya da tsohuwar kwamishinar sun yi dandazo ne domin kaura daga jam'iyyar APC zuwa PDP, AIT ta ruwaito.
Jiga-jigan na PDP sun ce, tashin hankalin da ake a jam'iyyar yanzu ba komai zai kara mata ba illa karfi gabanin babban zabe.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
'Yan Najeriya sun gaji da mulkin APC
Sun kuma bayyana kwarin gwiwar cewa, 'yan Najeriya sun gaji da mulkin APC.
Adeyanju, wacce ta kasance shugabar tawagar mata a fafutukar zaben gwamna Akeredolu a shekarun 2016 zuwa 2020, ta ce ba za ta iya kame baki tare da yaudarar kanta cewa APC na aiki tukuru ba.
Shugaban PDP na jihar, Fatai Adams ne da sauran jiga-jigai a jihar suka karbe su zuwa PDP, Daily Independent ta tattaro.
Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Gwamna PDP Na Jihar Ogun
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abeokua, babban birnin jihar Ogun ta soke zaben fidda gwanin gwamnan da jam'iyyar PDP ta gudanar a jihar.
A jihar Ogun, an samu tsaiko a PDP yayin da aka samu bangarori uku da suka gudanar da zaben fidda gwani daban-daban, The Nation ta ruwaito.
Daya daga ciki, ya samar da Hon. Ladi Adebutu a matsayin wacce ta lashe zaben, kuma ita za ta gwabza a babban zaben 2023.
Sai dai, mai sharia Oguntoyibo ya rushe zaben fidda gwanin, inda ya ba da umarnin sake sabon zaben a wani lokaci mai aminci a nan gaba cikin kwanaki 14, rahoton Tribune Online.
Asali: Legit.ng