Yadda Buhari da Atiku Suka Saba Dokar Kashe Kudi a Zaben Shugaban Kasa Inji INEC

Yadda Buhari da Atiku Suka Saba Dokar Kashe Kudi a Zaben Shugaban Kasa Inji INEC

  • Hukumar INEC mai gudanar da zabe a Najeriya ta zargi jam’iyyu da sabawa doka a lokacin zabukan 2019
  • Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu yace mafi yawan jam’iyyu ba su iya kawo rahoton kudinsu ba
  • A dokar Najeriya, duk wata jam’iyyar siyasa sai ta sanar da INEC abin da ta kashe a yakin neman zabenta

Abuja - Hukumar INEC mai gudanar da zabe tace APC da PDP da wasu jam’iyyu ba su gabatar da rahoto a kan kudin da suka batar a zabukan 2019 ba.

A wani rahoto da ya fito daga Daily Trust, shugaban hukumar INEC ta kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya yi jawabi a wajen wani taro a garin Legas.

An shirya wannan taron fadakarwa na kwana biyu da nufin wayar da kan manema labarai a kan shirye-shiryen zabe da aiki da sabuwar dokar zabe.

Kara karanta wannan

Atiku Yace 'Yan Kabilar Ibo Zai Mikawa Mulki Idan Ya Kammala Wa'adinsa

Aminu Idris wanda shi ne Darektan kula da harkar zabe da jam’iyyu, ya wakilci shugaban hukumar.

Jam'iyyu 57 ba su kawo rahoto ba

Idris a madadin Farfesa Yakubu yace a jam’iyyu 91 da suka shiga zabe, 34 ne kadai suka kawo rahoton kudin da suka batar da abin da suka samu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Babban jami’in na INEC yace a cikin jam’iyyu 34 da suka yi abin da doka tace, babu manyan jam’iyyun siyasar kasar nan, ma’ana irinsu APC da PDP.

Zaben Najeriya
Zaben Najeriya Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Za a horas da ma'aikata miliyan 1.4

Da yake gabatar da jawabinsa, shugaban cibiyar harkar zabe, Sa’ad Idris yace za su horar da ma’aikatan wucin gadi miliyan 1.4 domin aikin zaben 2023.

Leadership ta rahoto Idris yana cewa wadanda za a ba horaswa na musamman sun hada da malaman zabe da kuma jami’an tsaro da za ayi amfani da su.

Kara karanta wannan

Bayan Atiku Ya Kammala Wa'adin Mulkiinsa, Kudu Maso Gabas Ce Zata Samar da Shugaban Kasa, Jigon PDP

A ka’ida ya kamata hukumar INEC ta san nawa ne kudin da ya shiga hannun duk wata jam’iyya da kuma diddikin abin da ta kashe da sunan takara.

APC, PDP sun saba doka a zaben 2019?

Ana lissafin manyan jam’iyyun sun batar da Naira Biliyan 3.3 zuwa Naira Biliyan 4.6 wajen buga allo da yada talla a kafafen labarai a zaben da ya gabata.

Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar suka rikewa APC da PDP tuta a 2019. A lokacin Naira Biliyan 1 ne iyakar kudin da za a iya kashewa a kamfe.

Yau ake fara yakin neman zabe

Kuna da labari cewa Atiku Abubakar ya shiryawa yakin neman shugaban kasa, amma har yanzu Rabiu Kwankwaso bai fitar da kwamitin takara ba.

A halin yanzu, shi kuma ‘Dan takaran jam’iyyar APC mai mulki watau Bola Tinubu da Kashim Shettima duk suna kasar waje, ba su fara shirin kamfe ba.

Kara karanta wannan

Wani Sabon Hasashe Ya Tabbatar da Tinubu, Atiku Ba Za Su Lashe Zaben 2023 ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng