2023: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin PDP Na Takarar Sanata a Jihar Kebbi
- Babbar Kotun tarayya a Birnin Kebbi ta soke zaɓe na biyu da ya ba tsohon gwamna, Adamu Alieru, tikitin takarar Sanata a PDP
- Da yake yanke hukunci, Mai shari'a Ashgar, yace zaɓen farko da PDP ta gudanar lokacin Alieru na APC ingantacce ne
- Haruna Sa'idu, wanda ya lashe tikitin PDP a mazaɓar sanatan Kebbi ta tsakiya ya kai ƙarar Admu Alieru, PDP da INEC kan sauya sunansa
Kebbi - Babbar Kotun tarayya dake zama a Birnin Kebbi, Jihar Kebbi, a ranar Talata, ta yi watsi da zaben tsohon gwamnan jihar, Adamu Alieru, a matsayin ɗan takarar Sanatan Kebbi ta tsakiya a inuwar PDP.
Alƙalin Kotun, mai shari'a Babagana Ashigar, ya yanke hukuncin yadda mai ƙara Haruna Sa'adu ya nema, wanda ya tabbatar da cewa shi ne halastaccen ɗan takarar PDP a mazaɓar.
Premium Times tace Mista Saidu ya kai ƙarar Alieru, Sanatan Kebbi ta tsakiya mai ci, jam'iyyar PDP da hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) bisa gudanar da sabon zaɓen fidda gwani.
Ya shaida wa Kotun cewa sabon zaɓen ya saɓa wa kundin dokokin zaɓe 2022. Ya ƙara da cewa yana raye kuma bai janye daga takara ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Haka nan kuma ya yi iƙirarin cewa ƙarfa-karfa aka masa aka take doka wajen sauya sunansa da na Alieru, wanda ya sauya sheƙa daga APC zuwa PDP bayan an riga an gudanar da zaɓen fidda gwani.
Yadda Kotu ta yanke hukunci
Bayan kammala sauraren kowane ɓangare, Mai shari'a Ashigar yace ya fahimci cewa lokacin zaɓen farko da jam'iyyar PDP ta shirya Sanata Alieru yana cikin jam'iyyar APC.
Alƙalin ya yanke cewa bisa la'akari da shaidu na 2, 21, 23, 24 da aka gabatar wa Kotu, Haruna Sa'adu ya fafata a zaɓen farko inda aka zaɓe shi a matsayin ɗan takara bayan ya samu kuri'u mafi rinjaye.
"Ba Kuskure Bane" Jam'iyyar APC Ta Faɗi Dalilin Sanya Jigon PDP a Kamfen Tinubu, Ta Maida Martani Ga Gwamnoni
Alkalin yace:
"Tun da wanda ake ƙara na farko bai musanta zaɓen fidda gwanin farko ba, a gani na zaɓen fidda ɗan takarar Sanatan Kebbi ta tsakiya da aka gudanar da farko ya inganta, saboda haka kotu ta amince da rokon wanda ya kawo ƙara."
Zamu yi nazari kan hukuncin Kotu - Sanata Alieru
Da yake tsokaci kan hukuncin da Kotu ta yanke, Lauya Sanata Alieru, Aliyu Hassan, yace wanda yake kare wa zai yi nazari kan hukuncin kafin ɗaukar mataki na gaba.
A ɗaya bangaren, Lauyan Sa'idu, Sule Usman (SAN), yace hukuncin shi ne mafi kyau ga mutanen mazaɓar Kebbi ta tsakiya, yanzu sun san waye halastaccen ɗan takarar PDP, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
A Wani labarin kuma kun ji cewa Gwamnan PDP Ya Yi Watsi da Atiku Yayin da Ya Kai Ziyara Kudu Maso Gabas
Gwamnan jihar Abiya, Okezie Ikpeazu, ya yi watsi da zuwan Atiku yankin kudu maso gabas, bai halarci wurin taron ba.
Mai neman shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar, ya kai ziyara Enugu domin gana wa da masu ruwa da tsakin jam'iyya na yankin.
Asali: Legit.ng