El-Rufai Ya Girgiza da Jin Abin da Peter Obi Yake Fada Domin Jawo Kuri’un Kiristoci
- Ayekooto Akindele ya dauko wani bidiyo inda Peter Obi yake yi wa kiristoci jawabi a cocin Najeriya
- Dama irinsu ‘Dan takaran mataimakin shugaban kasa na PDP sun zargi Obi da sa addini a siyasar 2023
- Da El-Rufai ya saurari wannan bidiyo, ya nuna mamakinsa, sauran mutane suna ta tofa albarkacinsu
Lagos - Ayekooto Akindele ya dauko wani fai-fen bidiyo inda aka ji Peter Obi yana jawabi a coci, ya na nunawa kiristoci cewa su tashi tsaye.
Ayekooto Akindele wanda rikakken masoyin Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki ne, ya zargi ‘dan takaran LP da amfani da addini a siyasa.
A wannan gajeren bidiyo da yake yawo a Twitter, Obi ya fadawa mabiya addinin kirista cewa mutanensu ne ‘yan bindiga suke yin gaba da su.
Haka zalika ‘dan siyasar yace daliban da yajin-aikin da ake yi a jami’o’in gwamnati ya shafa, kiristoci ne, amma duk da haka jama’a sun yi gum.
Akindele ya na mai raddi da gatse a shafinsa, ya nuna lamarin rashin tsaro da yajin-aikin da kungiyar ASUU take yi ya shafi Musulmi da Kirista.
El-Rufai ya ga bidiyon
Daga cikin wadanda suka yi magana da ganin wannan bidiyo akwai Mai girma Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai wanda jigo ne a jam’iyyar APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malam Nasir El-Rufai bai yi doguwar magana ba, illa iyaka ya nuna matukar mamakinsa.
“Lallai!!! Shikenan!!! Madalla!!!
- Nasir El-Rufai
Kafin yanzu, an samu takaddama tsakanin Nasir El-Rufai da wasu magoya bayan Peter Obi da suka nemi suyi tattakisu a jihar da yake mulki.
Abin da Peter Obi ya fada
“A duk fadin Najeriya akwai mutanenku. Wadanda ake yin garkuwa da su, mutanenku ne. Ba zai yiwu ku zura idanu, har sai komai ya tabarbare ba.
Wadannan yara da ya kamata suna karatu, amma an rufe jami’o’i na watanni bakwai, yaran cocinku ne, kuma babu wani wanda ya damu da su.”
- Peter Obi
Obi yana kan gaba a hasashe
Rahoto ya zo dazu cewa a wani bincike da nazari da Gidauniyar We2Geda Foundation ta shirya, ta fahimci takarar Peter Obi a zaben 2023 tayi karfi.
A cikin mutane sama da 15, 000 da aka yi magana da su a jihohi 36, kimanin 8700 sun ce Jam’iyyar LP za su zaba, kusan 45% suke tare da PDP da APC.
Asali: Legit.ng