Wani Sabon Hasashe Ya Tabbatar da Tinubu, Atiku Ba Za Su Doke LP a Zaben 2023 ba
- Idan hasashen We2Geda Foundation ya tabbata gaskiya, Peter Obi ne zai zama shugaban kasar Najeriya
- Gidauniyar We2Geda Foundation tayi nazari a kan mutane 15, 000 domin jin wanda za su zaba a 2023
- Fiye da 50% na wadanda aka yi magana da su, sun nuna kuri’arsu tana wajen Peter Obi na jam’iyyar LP
Nigeria - Yayin da ake shirin fara kamfe na zama shugaban kasa a Najeriya, ana fahimtar Peter Obi yana kara karfi tsakanin ‘yan takaran 2023.
Wani hasashe da gidauniyar We2Geda Foundation ta gudanar ya nuna Peter Obi ne a kan gaba. Daily Trust ta kawo wannan labari a safiyar Talata.
Hasashen We2Geda Foundation ya nuna cewa a cikin manyan ‘yan takaran shugabancin Najeriya, Peter Obi na jam’iyyar LP shi ya fi karbuwa.
A cikin mutane fiye da 15, 000 da aka yi wa tambaya, 51% sun nuna Obi za su ba kuri’arsu a zaben 2023. Za a iya samun cikakken rahoton a nan.
Rahoton yace We2Geda Foundation tayi wannan hasashe a jihohi 36 da ke kasar nan da kuma birnin tarayya ta hanyar kiran mutane ta wayar salula.
Masu yin binciken sun yi amfani da harsunan da mutane suka fahimta wajen jin ra’ayoyinsu a game da wanda za su zaba ya zama shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda aka tuntuba sun fito ne daga kauyuka zuwa birane, sannan an yi la’akari da jinsi da kuma shekarun wadanda ake jefawa wadannan tambayoyi.
Yadda muka yi aikin - Abdulkareem Obioha
Abdulkareem Muna Obioha ya fitar da jawabi a madadin gidauniyar, ya yi bayanin adadin mutanen da suka zanta da su daga kowace jiha da ke Najeriya.
Tambayoyin da ake yi wa jama’a sun hada da; ‘Za ku yi zabe?’ ‘Kun mallaki katin PVC?’ ‘Menene matsalolin da ake fuskanta?’ ‘Wace jam’iyya za ku zaba?’
Zabin mutane ya ta’allaka ne da inganta tsaro, yaki da rashin gaskiya, samar da ayyukan yi, sai kuma farfado da ilmi wanda yake da alaka da ASUU.
Sakamakon nazarin da aka yi
Peter Obi ya samu 51%, sai 25% suka ce Alhaji Atiku Abubakar za su zaba, sannan 19% suka nuna suna goyon bayan Bola Tinubu na jam’iyyar APC.
3% sun zabi Rabiu Kwankwaso, sai ragowar suka zabi wasu 'yan takaran na daban.
Kamar yadda Muna Obioha ya bayyana, Obi yayi karfi a duka yankunan Kudu da Arewa maso tsakiya, jam’iyyar PDP ta fi karfi a ragowar Arewa.
Lissafin 2023 ya hada Peter Obi da Obasanjo
An samu labari 'dan takaran LP, Peter Obi da Olusegun Obasanjo sun sa labule a karo na 3 a cikin watanni 3 domin shiryawa zaben shugaban kasa.
Bayan ya ziyarci tsofaffin shugaban Najeriya a Minna, an ga ‘Dan takaran shugaban kasar a gidan Obasanjo wanda ya sauka daga mulki a 2007.
Asali: Legit.ng