Shugaba Buhari Ya Fadi Gaskiya Kan Kishin-Kishin Din Ya Nemi a Tube Keyamo Daga Kamfen Din Tinubu

Shugaba Buhari Ya Fadi Gaskiya Kan Kishin-Kishin Din Ya Nemi a Tube Keyamo Daga Kamfen Din Tinubu

  • Fadar shugaban kasa ta magantu a kan rade-radin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi a cire Festus Keyamo a kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC
  • Kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya bayyana ikirarin a matsayin karya mara tushe balle makama
  • Ya bayyana cewa daga Buhari har Bola Ahmed Tinubu suna farin ciki da aikin da karamin ministan ke yi

Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi watsi da rahotannin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi a tsige Festus Keyamo daga matsayin kakakin kwamitin kamfen din dan takarar shugaban kasa na APC.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu ya bayyana ikirarin a matsayin kanzon kurege.

Buhari da Keyamo
Shugaba Buhari Ya Fadi Gaskiya Kan Kishin-Kishin Din Ya Nemi a Tube Keyamo Daga Kamfen Din Tinubu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shehu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya saki a yammacin ranar Litinin, 26 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

2023: Rawar Da Nake Takawa Na Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a Sirrince, Saraki Ya Magantu

Ya rubuta a shafinsa na twitter:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Labarin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga tsige Festus Keyamo, SAN a matsayin kakakin kungiyar kamfen din shugaban kasa na APC labarin karya ne.
“Daga shugaba Buhari hard an takarar shugaban kasa, Asiwaku Bola Ahmed Tinubu suna farin ciki da aikin da Keyamo yake yi, da kuma yadda ake shirin kaddamar da yakin neman zabe mai zuwa, wanda tuni ya zama abin koyi ga sauran jam’iyyu.
"Muna sane da cewa ana shirya makirci don bata sunan shugabannin jam'iyyarmu da kuma garkame yakin neman zaben. Kada magoya bayan yan takararmu su damu da "labarai" daga wadannan masu watsa labaran karyan.”

Yan Najeriya Na Fama Da Matsanancin Yunwa Ta Yadda Basa La'akari Da Addinansu A Zaben 2023 - Jigon APC

A wani labarin, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Festus Keyamo, ya ce yan Najeriya na fama da tsananin yunwa da basa la’akari da addininsu a zabin da za su yi a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Barin Najeriya, Masoyan ‘Dan Takara Sun Fito da Shirin da Suke yi

Mista Keyamo ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talbijin na Channels a daren ranar Lahadi, kan sukar da ke ci gaba da fitowa daga tikitin Musulmi da Musulmi na jam’iyyar.

Jam’iyyar APC ta tsayar da Bola Tinubu, wanda yake Musulmi daga kudu maso yamma da Kashim Shettima, Musulmi daga arewa maso gabas a matsayin yan takararta na shugaban kasa da mataimakin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng