Allah Bai Gaya Mun Magajin Buhari Ba, Malamin Addini Ya Magantu Kan Zaben 2023

Allah Bai Gaya Mun Magajin Buhari Ba, Malamin Addini Ya Magantu Kan Zaben 2023

  • Babban limamin coci, Fasto William Kumuyi, ya bayyana iya abun da ya sani game da wanda zai zama shugaban kasa a 2023
  • Shugaban cocin na Deeper Christian Life Ministry ya ce Allah bai gaya masa wanda zai zama magajin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ba
  • Sai dai ya yi alkawarin sanar da jama'a halin da ake ciki da zaran Allah ya sanar da shi game da wanda zai lashe zabe mai zuwa

Minna, Niger - Babban limamin cocin Deeper Christian Life Ministry, Fasto William Kumuyi, ya bayyana cewa Allah bai yi masa wahayi game da wanda zai zama shugaban kasar Najeriya na gaba ba.

Sai dai kuma ya yi alkawarin bayyanawa duniya da zaran Allah ya sanar da shi wanene shugaban kasar Najeriya na gaba, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Su Dakatar Da Ni Idan Za Su Iya, Wike Ya Yi Wa PDP Barazana

Kumuyi
Allah Bai Gaya Mun Magajin Buhari Ba, Malamin Addini Ya Magantu Kan Zaben 2023 Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Kumuyi ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, jihar Neja yayin wani taro da ya gudana a ranar Lahadi, 25 ga watan Satumba.

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Ba zan gaya maku karya ba. Allah bai nuna mun komai ba. Bai ga dacewar fada mani ba. Baya so ya sanar da kowa, komai. Wanene ni da zan ce ma Allah, me yasa baka fada mani shugaban kasa nag aba ba? Idan ya sanar da ni, zan fito na fada maku."

Ya kuma yi kira ga matasan da suka kai shekarun zabe da su fito a ranar zabe sannan su zabi yan takarar da suke muradi wadanda suke ganin za su kai Najeriya matakin da take fatan kaiwa, Nigerian Tribune ta rahoto.

Babban faston ya ce zama ayi sulhu shine zai kawo karshen rikici tsakanin malaman jami’o’I da gwamnatin tarayya da kuma komawar dalibai makaranta yana mai cewa zuwa kotu, yin barazana da zanga-zanga ba shine maslaha ba.

Kara karanta wannan

Ba Buhari Bane Matsalar Najeriya, Ku Dena Dora Masa Laifi, In Ji Babban Malamin Addini

Shugaban Kasa A 2023: Wasu Manyan Gwamnonin Arewa 3 Na Shirin Marawa Peter Obi Baya

A wani labarin kuma, mun ji cewa gabannin babban zaben shugaban kasa na 2023, an rahoto cewa wasu manyan gwamnonin arewa uku sun nuna ra’ayinsu na son marawa kudirin Peter Obi baya.

Jaridar The Cable ta rahoto cewa, Kayode Ajulo, wani mai rajin kare hakkin dan adam ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a, 23 ga watan Satumba, lokacin da ya zanta da manema labarai a Abuja.

Sai dai kuma, Ajulo bai ambaci sunayen wadannan gwamnoni da yace suna shirin marawa takarar shugabancin tsohon gwamnan na Anambra baya ba.

Asali: Legit.ng

Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel