Hotuna: Peter Obi Da Abokin Takararsa Baba-Ahmed Sun Ziyarci Sarkin Kano, Ya Bayyaan Abin Da Suka Tattauna

Hotuna: Peter Obi Da Abokin Takararsa Baba-Ahmed Sun Ziyarci Sarkin Kano, Ya Bayyaan Abin Da Suka Tattauna

  • Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party, ya ziyarci Kano a yunkurinsa na samun goyon bayan yan arewa gabanin zaben 2023
  • Obi, tare da abokin takararsa Datti Baba-Ahmed, ya ziyarci Sarkin Kano Mai martaba Aminu Ado Bayero a ranar Asabar 24 ga watan Satumba
  • Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce ya yi tattaunawa mai amfani da sarkin na Kano

Kano - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, Peter Obi da abokin takararsa Datti Baba-Ahmed sun ziyarci Mai Girma Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Obi, wanda ya wallafa rubutu da hotuna a shafinsa na Twitter a ranar Asabar ya ce 'an yi tattaunawa masu muhimmanci' tare da sarki.

Peter Obi ya ziyarci Sarkin Kano
Hotuna: Peter Obi Da Abokin Takararsa Baba-Ahmed Sun Ziyarci Sarkin Kano, Ya Bayyaan Abin Da Suka Tattauna. Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan na Jihar Anambra ya rubuta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Magana Bayan Fallasar Wike, Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Ci Zabe A 2023

"Na ziyarci kasar Kano mai dumbin tarihi tare da abokin takara na, Yusuf Baba-Ahmed. Na samu damar ziyarar Mai Martaba Sarkin Kano Aminu Ado Bayero."

Obi kuma ya ziyarci Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Ibrahim kuma ya tattauna game da gobarar da ya faru a kasuwa da ambaliyar ruwa a Kano.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya rubuta:

"Mun tattauna abubuwa masu muhimmanci da amfani, ciki har da gobarar da ta faru a kasuwar Kano da ambaliyar ruwa a arewa."

A bangare guda, yanayin shigar da Peter Obi ya yi ya dauki hankalin wani mai amfani da Twitter, Thεό Abu, @TheoAbuAgada, wanda ya ce bai ji dadin hakan ba.

Ya rubuta:

"Mai yasa wani zai ba wa Obi babban rigarsa domin ya dauki hoto ya yi kama da dan arewa?
"Wannan ba daidai bane kuma ya kamata a soki abin. A bar Obi ya zama Obi kuma a dena tilasta shi ya saka tufafin da bai saka daga gida ba. Ban ji dadi ba."

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Sunayen Jaruman Fina-Finan Najeriya 24 Da Suka Samu Shiga Kwamitin Kamfen Din Tinubu

2023: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Karar Da PDP Ta Shigar Na Neman Haramtawa Tinubu Da Obi Yin Takara

A wani rahoton, babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta yi watsi da karar da jam'iyyar PDP ta shigar na neman a soke takarar Bola Tinubu na jam'iyyar APC da Peter Obi na Labour Party, The Cable ta rahoto.

A karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1016/2022, PDP ta kallubalanci sauya yan yan takarar mataimakan shugaban kasa da APC da Labour Party suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164