Jigon Jam'iyyar PDP da Mambobi 200 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Delta

Jigon Jam'iyyar PDP da Mambobi 200 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Delta

  • Jigon Jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Delta ya jagoranci ɗaruruwan mambobi sun koma jam'iyyar APC ranar Asabar
  • Prince Gabriel Nwanazia, yace ya ɗauki matakin koma wa APC ne saboda rikicin da PDP ke fama da shi wanda ya ƙi kare wa
  • Kansila ɗaya tilo na APC a faɗin jihar Delta yace wannan sauya sheƙa wata alama ce dake nuna karshen PDP

Delta - Ɗaya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar PDP mai mulki a jihar Delta, Prince Gabriel Nwanazia, ya sauya sheƙa tare da mambobi sama da 200 zuwa jam'iyyar APC.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Nwanazia, wanda ya tabbatar da koma wa APC a ƙaramar hukumar Aniocha ta arewa tare da ɗumbin magoya bayansa, yace ya ɗauki matakin ne sakamakon rikicin PDP da ya ƙi ci ya ƙi cinye wa.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP Na Tura Mummunan Sako Ga Yan Najeriya Game da Zaɓen 2023, Wike

Sauya shekar yan siyasa a Najeriya.
Jigon Jam'iyyar PDP da Mambobi 200 Sun Sauya Sheka Zuwa APC a Jihar Delta Hoto: punchng.com
Asali: UGC

A Jawabinsa yace, "Ni ɗan a mutun PDP ne kuma mamba amma yau na yanke tattara masoyana sama da ɗari biyu zuwa jam'iyyar APC."

"Jam'iyyar PDP ba ta da cika alƙawari, na yi wa jam'iyyar aiki tsawon shekaru, na ja ragamar jam'iyyar zuwa nasara a kowane zaɓe a yankin ƙaramar hukumar Aniocha ta arewa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Amma duk da haka yau, babu wani cigaba da muka samu a yankin mu, wasu abubuwa da kuke gani a nan duk APC ce ta yi su. Ga kuma uwa uba rikici da ya addabi PDP."

Karshen PDP ya zo a jihar Delta

Da yake gabatar da masu sauya sheƙar ga shugabannin APC, Kansila ɗaya tilo da APC ke da shi a jihar Delta, Emmanuel Oweazim, yace Mista Nwanazia ya kasance karfen ƙafa ga APC a zaɓukan baya.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: ASUU Ta Maida Martani Kan Hukuncin Kotu Na Janye Yajin Aiki

"2023 lokaci ne da zamu ɓinne PDP a jihar Delta, ɗaya daga cikin masu bamu matsala a yanzu ya dawo cikinmu kuma muna sa ran mutane da yawa zasu shiga APC nan gaba kaɗan."
"Rikici ya janyo PDP ta rasa ɗaya daga cikin jiga-jiganta kuma daga lokacin da Omo-Agege ya lashe zaɓe, ba zan zama ni kaɗai ne Kansilan APC a jiha ba."

Da suke karɓan masu sauya shekar, shugaban APC na yankin Aniocha ta arewa, Mr. Mathew Chinye, da ɗan takarar majalisar jiha, Mr. Bazim Boise, sun ce sauya sheƙar shugaban matasa Nwanazia alama ce ta karshen PDP a Delta.

A wani labarin kuma Atiku Ya Kara Shiga Tsaka Mai Wuya, Wasu 'Ya'yan PDP a Arewa Sun Koma Tsagin Wike

Wasu matasan jam'iyyar PDP a arewa sun koma bayan tsagin Gwamna Nyesom Wike, inda suka nemi lallai sai Ayu ya yi murabus daga kujerar shugabancin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Bayan Su Wike, Wasu Kusoshin Siyasa a Tafiyar Atiku Sun Koma Bayan Tinubu a Zaɓen 2023

Matasan wadanda suka gudanar da zanga-zanga a a Kaduna sun bayyana cewa PDP ba jam'iyyar arewa bace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262