A kai kasuwa: Jam’iyya ta ba ‘Dan Majalisa Takara, Amma Ya Yi Watsi da Tikitinta

A kai kasuwa: Jam’iyya ta ba ‘Dan Majalisa Takara, Amma Ya Yi Watsi da Tikitinta

  • Hon. Toby Okechukwu ya yi martani da ya ga sunansa ya fito a wadanda za a gwabza da su a zaben 2023
  • Okechukwu ya fitar da jawabi yana mai tabbatar da ba zai yi takarar 'dan majalisa a inuwar Labour Party ba
  • ‘Dan siyasar yace har gobe yana nan a PDP, bai karbi tayin Labour Party na takarar majalisar tarayya ba

Abuja - Mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Hon. Toby Okechukwu ya nesanta kansa daga takara a Labour Party.

This Day tace Honarabul Toby Okechukwu ya yi magana bayan ya ga sunansa a matsayin ‘dan takarar ‘dan majalisar tarayya a jam’iyyar LP.

A wani jawabi da ya fitar a ranar Laraba, ‘dan majalisar tarayya ya bayyana cewa ba zai nemi takarar wata kujera a zaben shekara mai zuwa ba.

Kara karanta wannan

Jigon PDP Ya Kara Ja Da Baya da Atiku, Yace Babu Tabbas a Kan ‘Dan Takaransu

Baya ga haka, Toby Okechukwu ya tabbatar da cewa bai da niyyar barin jam’iyyarsa ta PDP.

"Na sanar da LP ba zan yi takara ba"

Kamar yadda ya fada, ‘dan siyasar yake cewa ya sanar da shugaban jam’iyyar LP na kasa ba zai shiga yakin neman zabe da tutar da suka ba shi ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Leadership tace INEC ta fitar da sunan shi a matsayin wanda zai yi wa Labour Party takarar ‘dan majalisa na shiyyar Awgu/Oji-River/Aninri a Enugu.

‘Dan Majalisa
Wasu 'Yan Majalisar Wakilai a Najeriya Hoto: HouseNgr
Asali: Twitter

Fitaccen ‘dan siyasar yana cikin mutane sama da 4200 da sunansu suka shiga cikin ‘yan takaran majalisar dattawa da na wakilan tarayya a 2023.

Jawabin da aka fitar

“Na samu labarin hukumar INEC ta wallafa sunayen masu shiga takara a zaben 2023 a ranar 20 ga watan Satumba, 2022, inda sunana ya fito a matsayin ‘dan takarn LP na shiyyar Aninri/Awgu/Oji River, jihar Enugu a majalisar wakilan tarayya.

Kara karanta wannan

Rigimar Takara: An Kai Shugaban Jam’iyyar PDP da Jagororin Jam’iyya Gaban IGP

Ina so in shaida cewa ba zan yi takara a karkashin LP ko wata jam’iyya a wannan zabe ba. Ina nan a matsayin ‘dan jam’iyyar PDP.”
Na sanar da shugaban jam’iyyar LP na kasa a kan wannan matsaya a wata wasika da na aika masa tun a ranar 19 ga watan Yuli 2022.
Nayi matukar godiya da kaunar da shugabanni da daukacin mutanen mazabata suka nuna mani, da neman ganin na shiga takara a zabe.
Na fahimci hakan ba za iyi masu dadi ba, amma ina mai tabbatar masu da cewa zan cigaba da yin bakin kokarina wajen bada gudumuwa."

Fasto ya ba kiristoci satar amsa

A makon nan ne aka ji labari Fasto Samuel Oladele yace dole ne Kiristoci su maida hankalinsu a kan zabe mai zuwa, ba za ayi wasa da siyasar 2023 ba.

Babban Faston mai jagorantar Christ Apostolic Church (CAC) Worldwide yace a ajiye duk wata alaka, ayi la’akari da addini wajen zaben wanda zai yi mulki.

Kara karanta wannan

Tsohon SGF a Mulkin Buhari da Wani Jigon APC Sun Sha Alwashin Yakar Tinubu/Shettima a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel