Rikicin PDP: Wani Gwamnan Arewa da Ayu suka Kitsawa Wike Kullaliya inji Jang
- Sanata Jonah Jang yace akwai shirin da aka yi tsakanin Iyorchia Ayu da Aminu Waziri Tambuwal a PDP
- Tsohon gwamnan jihar Filato yace shugaban jam’iyyar PDP ya yi niyyar hana Nyesom Wike samun tikiti
- Jang ya kafa hujja ne da yadda Ayu ya taya Gwamna Tambuwal murnar kawowa Atiku Abubakar nasara
Rivers - Tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang ya fito yana zargin shugaban PDP na kasa, Iyorchia Ayu da yin wani shiri da Aminu Waziri Tambuwal
Premium Times ta rahoto Sanata Jonah Jang yana cewa tun farko an shirya yaudarar Gwamna Nyesom Wike da masu neman tikitin shugaban kasa.
Sanatan na jihar Filato ya bayyana wannan ne a ranar Laraba, 21 ga watan Satumba 2022, inda suka yi wani zama a gidan gwamnan na Ribas da ke Fatakwal.
A cewar tsohon gwamnan, Iyochia Ayu ya zama tamkar alkalin wasa da ya taimakawa ‘yan wasa wajen zura kwallo a raga, sai ya hura tashin wasa.
Da walakin inji su Wike
Jang yace idan har Ayu a matsayinsa na shugaban jam’iyya, zai je ya rungumi Aminu Tambuwal bayan zaben tsaida gwani, ya nuna akwai abin da suka shirya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Anyi Alkalin wasan da ya taimakawa wani bangare wajen cin kwallo, sai kuma ya hura tashi cewa an zura kwallo a raga.
Ba abin da ya sa muka kafa jam’iyyar PDP tayi wa mutanen Najeriya kenan ba, saboda shiyasa muke cewa Ayu ya sauka.”
- Jonah Jang
Bayanin da Jonah Jang ya yi, yana cikin wani bidiyo da gidan talabijin Channels TV ya wallafa.
Abin da ya faru a wajen takara
Abin da ya faru a zaben tsaida gwanin shi ne Aminu Tambuwal ya janye takararsa, ya nemi mutanensa su marawa Atiku Abubakar baya ya samu tikiti.
Magoya bayan Wike suna ganin ba ayi masu adalci ba domin janyewar gwamnan na Sokoto ta zo ne a lokacin da aka rufe kofa, ana shirin a fara kada kuri’u.
Tuni har ‘dan takaran na PDP ya nada Gwamna Tambuwal a matsayin Darekta Janar na kamfe, wasu suna ganin an yi masa sakayyan irin abin da ya yi ne.
Wike su dawo APC - FFK
Kun ji labari Femi Fani-Kayode yace ya san za a zo irin wannan rana a PDP, ya yi wa jam’iyyar kaca-kaca, kuma ya fadawa su Nyesom Wike su shigo APC.
Tsohon Ministan tarayyan wanda jama’a suka fi sani da FFK yace yanzu duk wanda ba ‘Dan Arewa ba, hoto ne a PDP, sam babu adalci a jam’iyyar da ya bari.
Asali: Legit.ng