Tun da Sulhu Ya Gagara, Jigon Jam’iyya Ya Shiga Zawarcin Abokan Fadan Atiku

Tun da Sulhu Ya Gagara, Jigon Jam’iyya Ya Shiga Zawarcin Abokan Fadan Atiku

  • Femi Fani-Kayode ya yi raga-raga da jam’iyyar PDP a wani dogon rubutu da ya yi a shafin Facebook
  • Tsohon jagoran na PDP yace jam’iyyar ta saki layi, yanzu an maida duk wani ‘Dan kudu tamkar hoto
  • Fani-Kayode ya ba Nyesom Wike da mutanensa shawara su hakura da zaman PDP, su bi Bola Tinubu

Abuja - Femi Fani-Kayode ya fadawa Gwamna Nyesom Wike cewa ya jefar da kwallon mangwaro, ya huta da kuda a rikicin cikin gidan PDP.

Legit.ng Hausa ta fahimci Cif Femi Fani-Kayode ya yi kira ga Nyesom Wike da ya tsallako zuwa jam’iyyar APC mai mulki domin a doke PDP a 2023.

Tsohon Ministan jiragen saman ya fitar da jawabin da ya yi wa take da: "A WORD FOR THE WIKE GROUP: LEAVE THE CARCASS AND STAND WITH US!”

Kara karanta wannan

Tsohuwar Jam’iyyar Atiku Ta Juya Masa Baya, Za Tayi Wa Tinubu Aiki a Zaben 2023

Za a iya cewa yace: “Kira ga ‘yan bangaren su Wike: Ku jefar da kwallon mangwaro, ku huta da kuda.”, inda ya dura kan shugabannin PDP na yau.

PDP ta tashi daga PDP a yau

Fani-Kayode ya rubuta wannan a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, yace yanzu PDP ba jam’iyyar ‘yan kasa bace, tayi watsi da ‘Yan siyasar Kudu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“A gaskiya ina tausayawa ‘yan bangaren Wike. Ana yi masu kallon kashi a jam’iyyarsu. Ba yadda suka iya, dole su fita daga yakin takarar Atiku.”
Nyesom Wike
Gwamnan Ribas, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Asali: Facebook
“Dama can na hano wannan tun tuni. Meyasa kuke tunanin na bar PDP tun farko? Jam’iyya ce da ba ta san kowa ba sai mutumin yankin Arewa.”
Duk wani ‘dan kudu ko ‘dan Arewa maso tsakiya ba kowan komai ba ne, hoto ne kurum.
Jam’iyya ce da ba ta yarda da muhimmancin hada-kai a zauna lafiya ba, ba ta yarda da kaunar da ke tsakanin Kudu da Arewa, da adalci ga kowa ba.

Kara karanta wannan

Wike Ya Rasa Ƙashin-Baya a Rikicin PDP, Na Hannun Damansa Yace Atiku Zai Yi Wa Aiki

Vanguard ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa a yanzu lemar da aka san PDP da ita a lokacin Obasanjo, ‘Yar’Adua, da Jonathan, cike take da tsutsotsi.

Babu abin da ya rage masu a PDP

“Abin da ya ragewa mutanen Wike shi ne su sauya-sheka, su goyi bayan Asiwaju a zaben shugaban kasa, su fadawa mabiyansu cewa su zabe shi.
Tun daga darajarsu, an karbe komai daga hannunsu. Me kuma ya rage masu? Me suke jira?

Tinubu ya samu karin goyon baya

Shugabannin Peoples Democratic Movement (PDM) da suka marawa Atiku baya a 2019, sun tsallako APC, a makon nan aka rahoto wannan.

Baya ga haka, ‘Yan kungiyar Muslim/Christian Youths & Elders Forum da na Genuine Governance Group (GGG) suna tare da Bola Tinubu a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng