Baya da kura: Atiku Ya Sheka Kasar Waje, Maganar Shawo Kan Rikicin PDP Ya Wargaje

Baya da kura: Atiku Ya Sheka Kasar Waje, Maganar Shawo Kan Rikicin PDP Ya Wargaje

  • Sulhun da ake neman ayi wa bangarorin Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike yana neman gagara
  • Alhaji Atiku Abubakar ya fusata mutanen Wike da ya nada Gwamnan Sokoto ya yi masa Darekta na kamfe
  • Sabon shugaban BOT ya yi damara, yana kokarin ganin ya sasanta kan ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayyar a ko ina

Abuja - Yunkurin da ake yi na ganin an sasanta bangarorin jam’iyyar PDP da ke rigima ya sukurkuce a halin yanzu, The Nation ta kawo wannan rahoto.

Sulhun Alhaji Atiku Abubakar da Gwamna Nyesom Wike ya tabarbare bayan da aka nada Aminu Waziri Tambuwal ya jagoranci yakin neman zaben PDP a 2023.

Matakan da aka dauka a jam’iyyar PDP a baya-bayan nan ba su dinke baraka ba. Mutanen Wike har sun fara lissafin matakin da za su dauka a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Tun Yanzu, Atiku Abubakar Ya Fara Tattara Sunayen Wadanda Zai Ba Mukamai

Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa Atiku Abubakar ya tura Ayo Fayose domin ya shawo kan Gwamnan Ribas, amma mutanen Wike ba su karbi maganar ba.

Ana tunanin akwai wani Gwamnan Arewa wanda yake tare da Wike da yanzu zai koma goyon bayan Atiku wanda ke takarar shugabancin kasa a zaben badi.

Har yanzu ‘dan takaran bai cika sharudan ‘yan bangaren Wike na sulhu ba. Daga ciki shi ne maye gurbin Iyorchia Ayu da wani ‘dan Kudu, an ki yin hakan har yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku
Atiku tare da matasa a Legas Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Rahoton ya nuna cewa, nada Adolphus Wabara a matsayin sabon shugaban BOT na Jam’iyyar PDP ba tare da an yi shawara da su ba, bai yi wa su Wike dadi ba.

Kan PDP ya rabu a Kudu maso yamma

Haka zalila duk da shugabannin PDP na jihohin Legas, Ekiti. Ogun da Ondo sun nuna suna tare Iyorchia Ayu, shugaban jam’iyyar na kasa na fuskantar barazana.

Kara karanta wannan

An Gwabza Yaki Tsakanin Boko Haram, ‘Yan ta’adda Sun Kashe Kansu da Kansu

Jam’iyyar PDP ta reshen Oyo, ba ta tare da Atiku Abubakar ta dage kan sai an sauke Iyorchia Ayu. Wannan shi ne matsayar Gwamna Seyi Makinde har gobe.

Ana haka ne sai jaridar Punch ta kawo rahoto cewa wani babba a tafiyar PDP ya yi zama da tsohon Ministan yada labarai, Farfesa Jerry Gana a garin Abuja.

BOT za ta hadu da Gwamnoni

A yau Litinin, tawagar BOT za ta hadu da Gwamna Ahmadu Fintiri da Gwamna Samuel Ortom. Daga nan za a yi zama da Gwamnan Oyo, Seyi Makinde.

Shugaban majalisar BOT, Sanata Adolphus Wabara yace daga yau zuwa gobe, za suyi wannan zama da nufin a kawo karshen rigingimun cikin gidan jam'iyya.

Obi ba zai iya ba - Oshiomhole

An ji labari tsohon shugaban jam’iyyar APC yace a lokacin da Peter Obi yana Gwamna, ‘Yan Bakassi Boys suka addabi jiharsa, bai iya yin komai ba.

Ganin cew da yake Gwamna a jihar Anambra, babu abin da ya tabuka, Adams Oshiomhole yace ‘Dan takaran LP ba zai iya kawo tsaro a kasar nan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng