Kwankwaso Ya Ci Taro a Kudancin Najeriya, Kwandon NNPP ya Shiga Neja-Delta

Kwankwaso Ya Ci Taro a Kudancin Najeriya, Kwandon NNPP ya Shiga Neja-Delta

  • Jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari ta kaddamar da ofishinta a mazabar kudancin jihar Delta
  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ci karo da dinbin mabiya yayin bude sabon sakatariyan a garin Warri
  • Masu nazarin siyasa sun yi mamakin ganin yadda NNPP ta ratsa shiyyar kudu maso kudancin Najeriya

Delta - ‘Dan takarar kujerar shugabancin kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyarar siyasa zuwa jihar Delta.

Jaridar Legit.ng Hausa ta fahimci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci yankin Warri da ke Delta a yammacin Asabar dinnan.

Rabiu Musa Kwankwaso da magoya bayansa sun samu kaddamar da sakatariyar jam’iyyar NNPP na shiyyar kudancin jihar Delta.

Hadimin tsohon gwamna, Saifullahi Hassan ya wallafa wannan labari a shafinsa na Twitter.

"A yau 17 ga watan Satumba, ‘Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar @OfficialNNPPng, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso (@KwankwasoRM) ya kaddamar da sakatariyar NNPP na Kudancin jihar Delta a hanyar Odion, Warri, jihar Delta.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Hadimin Gwamnan Kaduna da Mambobin APC Sama da 13,000 Sun Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Bude ofishin ya jawo dinbin mutane daga magoya bayan jam’iyya."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

- Saifullahi Hassan

'Dan takaran NNPP
'Dan takaran NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso a Warri Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Kwankwaso ya yi murna

Kwankwaso mai neman zama shugaban Najeriya a 2023 ya yi magana a dandalin Twitter, yace ya yi farin ganin jama’a wajen taron.

“Na yi farin ciki da na kaddamar da ofishin babbar jam’iyyarmu ta @OfficialNNPPng na mazabar Kudancin Delta, cikin dandazon taro a titin Odion a garin Warri.

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Da muka zanta da Saifullahi Hassan, ya shaida mana cewa Kwankwaso ya ba mutane mamaki da aka ga irin wannan dandazo a yau.

Hadimin yake cewa ‘dan takaran ya ci taro a Delta, a lokacin da ake yi masa kallon wanda tasirinsa bai wuce yankin Arewacin Najeriya ba.

NNPP da Delta ta Kudu

Tsohon Soja, Naval Commodore Omatsaye Nesiama mai ritaya shi ne wanda za iyi wa jam’iyyar NNPP takarar Sanatan Delta ta Kudu a 2023.

Kara karanta wannan

Yadda Kwankwaso Zai Lallasa Atiku a Arewa, Ya Ba Da Mamaki a Zaɓen 2023, Tsohon Ɗan Majalisa

A ‘yan kwanakin nan, an ji Nesiama yana ta neman goyon bayan ‘Yan kabilar ljaw, lsokos, ltsekiris, da Urhobos domin ya zama Sanata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng