2023: Manyan Malaman Addini 5 Da Suka Fito Fili Suka Bayyana Goyon Bayansu Ga Tinubu

2023: Manyan Malaman Addini 5 Da Suka Fito Fili Suka Bayyana Goyon Bayansu Ga Tinubu

Tun bayan nasarar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ya rika samun goyon baya da malaman addini a sassa daban na Najeriya.

Tsohon gwamnan na Legas ya zama wani tambari na siyasa da ke da magoya baya a bangarori daban-daban na kasar.

Kamar yadda ya ke da yan gani-kashe ni da masoya, wasu cikin manyan malaman addini sun nuna goyon bayansu ga Tinubun.

Bola Tinubu.
2023: Manyan Malaman Addini Guda 5 Da Suka Bayyana Goyon Bayansu Ga Tinubu. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga wasu fitattun malaman addini wadanda suka nuna goyon bayansu a fili ga Tinubu kamar yadda The Nation ta tattaro:

1. Prophet Isreal Oladele Ogundipe a.k.a Genesis - Bayan limamin cocin na CCC Genesis Global Parish, Isreal Oladele Ogundipe, ya fito karara ya goyi bayan Tinubu.

Kara karanta wannan

Al-Mustapha Ya Fashe Da Kuka Ya Zubar Da Hawaye Kan Rashin Tsaro A Najeriya

Malamin, yayin da ya ke yi wa magoya bayansa jawabi ya yi bayanin cewa yana goyon bayan Jagaban dari bisa dari saboda shi (Oladele) ba shege bane.

Oladele ya ce ko yana so ko baya so, ba zai taba barin dan kabilarsa ba ya zabi wani.

2. Bishop Kayode Williams - Wannan malamin addinin ya yi imanin cewa Tinubu ne zabin da Allah ya yi a matsayin shugaban kasa a 2023.

Shugaban cocin na Integrity Ministers International Ministries ya nuna goyon bayansa a fili ga Tinubu.

A hirar da shi da aka yi sau da yawa, ya ce:

"Idan ka kalli Bola Ahmed Tinubu, idan ka duba abin da ya yi a baya za ka san cewa mutum ne mai nazari sosai. Kafin ya dauki mataki kuma kafin ya fara, muna tare da shi.
"Amma Allah ya fada mana dan takararsa daga aljanna har duniya shine Tinubu kuma mu a Integrity Ministers International Ministries za mu mara masa baya mu hada hannu da shi, don haka muna tare da shi don sanin matakin da zai dauka."

Kara karanta wannan

NIN: Yadda Kujerar Minista Ta Jawowa Isa Ali Pantami Barazanar Kisa a Najeriya

3. Fasto Sunday Adelaja - Shine mai cocin Embassy of the Blessed Kingdom of God for All Nations Kyiv Ukraine.

Tuni dai Adelaja ya yi hasashen cewa dan takarar na APC, Asiwaju Bola Tinubu ne zai yi nasara.

Adelaja ya ce Tinubu zai yi nasarar zaman shugaban kasa a 2023 da tazarar kuri'u mai yawa.

Adelaja, a wani sako da ya wallafa a sahihin shafinsa na Facebook tsohon gwamnan na Legas zai yi nasara saboda wasu dalilai 10 da ya lissafa.

4. Fasto Alamu David - Shine bababn fasto na Christ Apostolic Church (CAC) a Abule Legas. Ya bayyana cewa Tinubu ne zai gaji Muhammadu Buhari a 2023.

Malamin, cikin sanarwar da ya fitar ya ce:

"Allah ya min wahayi a ranar 24 ga watan Yunin 2008 cewa mutum mai suna Bola Ahmed Tinubu zai mulki kasa, don cigaban Najeriya kuma na yi imanin cewa lokacin ya yi; 2023. 'Babu wanda zai dakatar da Baba".

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

5. Fasto John Desmond - Shugaban Young Professionals of Nigeria (YPN), Fasto John Desmond ya yi kira ga mutane su goyi bayan Tinubu.

Desmond ya yi wannan kiran ne a Umuahia, Abia yayin wani ziyara matasa kwararu wadanda mambobin APC ne a Kudu maso Gabas.

Desmond ya ce Tinubu yana da jarumta, hangen nesa da ikon iya sauya Najeriya.

Laifin Tinubu Ne "Idan Amaechi Ya Koma PDP", Babban Jigon APC Ya Fasa Kwai

A wani rahoton, Chukwuemeka Eze, fitaccen jagora a jam'iyyar APC kuma na hannun daman Rotimi Amaechi, tsohon ministan sufuri, ya ce a dora wa Bola Tinubu laifi idan Amaechi ya bar jam'iyyar.

Eze yana magana ne kan wani rahoto da ke ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar yana zawarcin Amaechi, The Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel