Dubbannin Mambobin Jam'iyyar APC a Kaduna Sun Koma Jam'iyyar PDP
- Jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kaduna ta gamu da gagarumar matsala yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen 2023
- Tsohon hadimin gwamna, Hon. Wilson Yangye da wasu mambobin sama da 13,000 sun koma PDP a kudancin jihar
- Shugaban PDP na jiha, Hon. Felix Hassan Hyat, yace tarihi zai cigaba da maimaita kansa game da kuri'un yankin a 2023
Kaduna - Mambobin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sama da 13,000 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a kudancin jihar Kaduna ranar Asabar.
Jaridar Punch tace Ma'ajiyin PDP reshen arewa maso yamma, Hon. Rabiu Bakori, shi ne ya karɓi masu sauya shekan a madadin shugaban PDP a shiyyar arewa-yamma Sanata Hayyatu Gwarzo.
A jawabinsa yayin taron sauya shekar wanda ya gudana a Zonkwa, Rabiu Bakori, yace wajibi kowa ya ba da gudummuwarsa idan har ana son PDP ta kai ga nasara a zaɓen 2023.
Yace, "Jam'iyya mai mulki ta mana alƙawarin inganta tsaro a 2015 amma bisa mamaki sai ta ƙare da dasa tsoro a zuƙatan yan Najeriya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ya zama tilas mutanen Kaduna su tashi tsaye su tabbatar jam'iyyar PDP ta kai ga madafun iko domin a musu adalci sannan kuma martabar demokaraɗiyya ta gaskiya ta dawo."
Kudancin Kaduna na PDP ne tun asali - Hayat
A ɓangarensa, shugaban PDP a Kaduna, Hon. Felix Hassan Hyat, ya ayyana sauya sheƙar mutanen da kyakkyawar alama kuma mai dumbin tarihi, inda ya ƙara da cewa zai taimaka wajen kai PDP gidan Sir Ƙashim Ibrahim a 2023.
"Babu wata jam'iyya dake samun nasarar zaɓe a kudancin Kaduna ban da PDP kuma a shekara mai zuwa, babu jam'iyyar da zata rusa wannan tarihin."
Masu sauya shekan bisa jagorancin tsohon babban hadimin gwamnan Kaduna, Hon. Wilson Yangye, sun yi alkawarin tattara kuri'un da zasu cicciɓa PDP zuwa nasara.
Mista Yangye, wanda ya taka muhimmiyar rawa har APC ta lashe ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da PDP ke da karfi, ya roki al'ummar yankin su yafe masa.
A wani labarin kuma Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa, Rabiu Kwankwaso, Ya Yi Kus-Kus da Wani Gwamnan APC
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, na jam'iyyar APC ya ziyarci tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Kwankwaso mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar NNPP yace ya karɓi bakuncin gwamnan ranar Laraba da daddare a Minna.
Asali: Legit.ng