Yan Jam'iyyar PDP 7000 Sun Sauya Sheka APC A Jihar Sakkwato

Yan Jam'iyyar PDP 7000 Sun Sauya Sheka APC A Jihar Sakkwato

  • Jam'iyyar APC Ta Samu gagarumin karuwar sabbin mambobi 7000 a jihar Sakkwato, Arewa maso yamma
  • Wadanda suka shiga jam'iyyar sun sauya sheka ne daga jam'iyya mai mulki a jihar, PDP
  • Wannan na faruwa lokacin da aka alanta Gwamnan Jihar Sokoto matsayin Dirakta Janar na yakin neman zaben Atiku

Yayinda zaben 2023 ke gabatowa, jam'iyyar All Progressives Congress APC ta samu gagarumin karuwa a jihar Sokoto.

Akalla yan jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP 7000 sun sauya sheka zuwa APC a makon nan.

Hakan na kunshe cikin jawabin da Bashar Abubakar, hadimin Sanata Aliyu Wammako ya fitar ranar Juma'a, rahoton Punch.

Jawabin ya biyo bayan sauya shekan da yan jam'iyyar PDP ke yi a jihar.

Masu sauya shekan sun samu kyakkyawan tarba daga wajen dan takaran gwamnan jihar, Ahmed Aliyu, a karamar hukumar Wurno ta jihar.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Ghali Na'Abba, Ya Sauya Sheka Zuwa PDP, Ya Fallasa Sirrin APC

Akalla mabiya PDP 4,270 suka koma APC a karamar hukumar, Bashar yace.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

APC Jam
Yan Jam'iyyar PDP 7000 Sun Sauya Sheka APC A Jihar Sakkwato
Asali: Twitter

Dan takaran gwamnan wanda ya wakilci Sanata Aliyu Wammako ya bayyana farin cikinsa bisa wannan karuwa da jam'iyyarsu ta samu.

Ya yiwa al'ummar garin alkawarin cewa idan suka zabesa, zai sake gina titin Huchi da ambaliyar ruwa ta lalata.

A cewarsa:

"PDP a jihar ta fadi warwas kuma bata cika alkawariko daya ckin wanda ta yiwa al'ummar jihar ba."

Tsohon Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Ya Fice Daga PDP, Yana Shirin Shiga APC

A wani labarin, tsohon ɗan takarar gwamna karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Yobe, Alhaji Abba Gana Tata, ya fice daga jam'iyyar ana shirin tunkarar babban zaɓen 2023.

Alhaji Tata ya bayyana matakin da ya ɗauka ne a wata wasika da ya aike ɗauke da adireshin shugaban PDP a ƙaramar hukumar Bursari da shugaban jam'iyya na jiha, Ambasada Umar El-Gadh.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

Jaridar Leadership ta ci karo da kwafin wasiƙar tsohon ɗan takarar gwamnan, wanda wani sashinta yace:

Asali: Legit.ng

Online view pixel