Tun Yanzu, Atiku Abubakar Ya Fara Tattara Sunayen Wadanda Zai Ba Mukamai

Tun Yanzu, Atiku Abubakar Ya Fara Tattara Sunayen Wadanda Zai Ba Mukamai

  • ‘Dan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP, Atiku Abubakar yana tattaro wadanda zai yi aiki da su a gwamnatinsa
  • Kakakin kwamitin PDP a zaben shugaban kasa, Charles Aniagwu, yace Atiku ya fara lissafin shiga ofis a 2023
  • Idan ‘dan takaran ya kai labari, zai jawo mutane ne daga kowace jam’iyya, har da masu aiki a kasashen waje

Abuja - Bisa dukkan alamu ‘dan takarar jam’iyyar hamayya ta PDP a zaben shugaban kasa na 2023, Atiku Abubakar ya hango alamun nasara tun a yanzu.

Charles Aniagwu ya yi hira da gidan talabijin na Arise TV, inda ya bayyana cewa Mai gidansa ya fara tattara sunayen wadanda zai ba kujeru a gwamnatinsa.

Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben na Atiku Abubakar ya tattauna da manema labarai a game da rikicin da ake fama da shi a jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan

2023: Jigon NNPP Ya Yi Hasashen Yadda Za Ta Kare da Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso

Kamar yadda Charles Aniagwu ya fada, idan har Atiku ya yi nasarar zama shugaban Najeriya a 2023, zai tafi da duk wanda ya kware a fanninsa a mulkinsa.

Hadimin ‘dan takaran yace Wazirin Adamawa ba zai yi la’akari da bangaren da mutum ya fito ko addini wajen raba kujeru ba, zai dauki kowa na shi.

Daily Trust ta bi wannan hira da aka yi, tace Atiku Abubakar zai raba mukamai har da wadanda ba ‘yan jam’iyyarsa ba, hakan ya nuna bai zai nuna gaba ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Atiku
Atiku Abubakar da Mai dakinsa Hoto: Atiku.org
Asali: Facebook

Yadda Atiku zai kafa gwamnati - Charles Aniagwu

“Duk inda ka ke, da zarar kana da rawar da za ka taka, Atiku Abubakar zai lalubo mutum a duk bangaren kasar nan da yake ko addinin da yake bi.”
“Shugaban kasa bai bukatar ya zama Likita kafin ya iya magance matsalar kiwon lafiya, bai bukatar zama Injiniya kafin ya duba matsalar gini.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Duk Da Ziyarar Atiku, Makinde Ya Ce Dole Ayu Yayi Murabus

Abin da shugaban kasa yake bukatar yi shi ne ya tattara mutane da suka san wadannan aiki. Yanzu da nake maganar nan, na san wasu ‘yan abubuwa.
Atiku ya fara rubuta sunayen wasu ‘Yan Najeriya da ke kasashen waje, da kuma wadanda ba su cikin jam’iyyarsa, wadanda yake so ya ba mukamai.”

Atiku mai jama'a

A cewar Aniagwu, idan za a gyara kasar nan, ba zai yiwu mutum ya dogara da ‘yan jam’iyyarsa kurum ba, yace Atiku yana da mutane a duk fadin Afrika.

Kwamishinan na jihar Delta ya yi watsi da zargin cewa Atiku zai fifita mutanensa.

Charles Aniagwu ya samu mukami

Kwanaki ku ka ji labari ‘Dan takarar kujerar shugaban Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bada sanarwar nadin mukami a kwamitin kamfe.

A lokacin aka ji Charles Aniagwu ya zama Kakakin kwamitin yakin neman takarar jam’iyyar PDP, zai yi aiki da Daniel Bwala da Dino Melaye a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Abin da Ya Sa Atiku Ya Yi Watsi da Wike, Ya Jawo Okowa Ya Zama Mataimakinsa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng