Ku Yi Watsi da Tinubu, Atiku da Obi, Shawarin Kwankwaso Ga ’Yan Najeriya

Ku Yi Watsi da Tinubu, Atiku da Obi, Shawarin Kwankwaso Ga ’Yan Najeriya

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ba da sako mai daukar hankali ga 'yan Najeriya gabanin zaben 2023
  • A bayaninsa, ya ce bai kamata 'yan Najeriya su bata lokaci wajen ba da kuri'unsu ga 'yan takarar APC, PDP da LP ba
  • Kwankwaso ya ce sam Tinubu, Atiku da Obi ba su tsinana komai ba da har za su iya rike ragamar Najeriya

Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso ya ba 'yan Najeriya shawari kyauta, ya su kiyayi kansu su yi watsi da 'yan takarar shugaban kasa a APC, PDP da LP.

Ya yi kira ga 'yan Najeriya da kada su zabi Bola Ahmad Tinubu, Atiku Abubakar ko Peter Obi a zaben 2023 mai zuwa, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ci gaba: Najeriya ta samu karuwa, Buhari ya ba Turawa da 'yan wasu kasashe shaidar zama 'yan Najeriya

A fahimtar Kwankwaso, ya kamata 'yan Najeriya su nisance 'yan takarar saboda basu da wani abin a zo a gani da za su iya ba kasar bayan an zabe su.

Kwankwaso ya caccaki abokan hamayyarsa
Ku yi watsi da Tinubu, Atiku da Obi, shawarin Kwankwaso ga 'yan Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Ku bar batun APC, PDP da LP, inji Kwankwaso

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da yake zantawa da manema labarai a birnin Minna a jiya Alhamis 15 ga watan Satumba, Kwankwasi ya ce 'yan takarar uku da ya ambata ba su da wani abu da zasu iya nunawa na kirki da har zai sa a zabe su, rahoton This Day.

Ya kuma kalubalanci 'yan takarar da su fito su fadawa duniya abin da suka yiwa Najeriya da yasa suka cancani gaje kujerar Buhari.

He urged them to present it to the world, what they have done for the country so far.

Kwankwaso ya caccaki APC da PDP

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya

Tsohon gwamnan na jihar Kano, ya kuma zargi APC da PDP da shafe shekaru 23 suna mulkin kasar, amma sun gaza sauya makomar kasar zuwa abin alfahari a duniya.

Ya kuma ce, a mulkin da suka shafe suna yi, har yanzu babu komai a Najeriya face rubabbun gine-gine da lalatattun ababen more rayuwa da ake amfani da zasu tsawon tarihin kasar.

Daga nan kuma ya shawarci 'yan Najeriya su zabi 'yan Najeriyan da suka cancanta ba wadanda suke ganin lokacinsu ne ya yi su yi shugabanci ba.

Najeriya Na Bukatar Tsarin Aikin Obasanjo, Karimcin Abacha da Jajircewar Buhari, Inji Kashim Shettima

A wani labarin, abokin takarar Tinubu a zaben 2023, Kashim Shettima ya bayyana abubuwan da kasar nan ke bukata daga shugaban da zai gaji Buhari a 2023 don kawo ci gaba a Najeriya, Punch ta ruwaito.

Da yake magana ranar Alhamis 15 ga watan Satumba bikin murna na 96 na kungiyar Yoruba Tennis Club da aka yi a Ikoyi ta Legas, Shettima ya ce Tinubu dan takarar da ya cika abin da ake bukata.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Bincike ya nuna wanda zai iya lashe zabe tsakanin 'yan takarar shugaban kasa 4

A cewar Shettima, Bola Ahmad Tinubu na jam'iyyar APC ne ya cika duk wasu abubuwan da ake bukata daga shugaban da ya cancanci hawa kujerar mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.