Tinubu Na da Tabbacin 80% Na Kuri’u a Kudu Maso Yamma a 2023, in Ji Kekemeke
- Jigon APC ya bayyana kwarin gwiwarsa na cewa Asiwaju Bola Ahmad Tinubu zai lashe zaben 2023 mai zuwa
- Mr Isaac Kekemeke ya ce Tinubu zai tabuka abin kirki a zaben, don haka zai kawo 80% na kuri'u
- Tawagar TAG ta bayyana cewa, za ta kawo shirye-shiryen da za su sa a dama da matasa a jam'iyyar APC
Akure, jihar Ondo - Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na a yankin Kudu maso Yamma, Mr Isaac Kekemeke ya bayyana kwarin gwiwarsa ga lashe zaben Tinubu a zaben 2023.
A cewarsa, akwai tabbacin dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu ya iya cin zabe da 80% a yankin Kudu maso Yamma, Daily Trust ta ruwaito.
Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya
Kodinetan tawagar 'The Asiwaju Group (TAG)' a jihar Ondo, Mr Olaniyi Adegbola ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da yace Kekemeke ne ya ba wannan tabbaci a Akure a jiya Laraba 14 ga watan Satumba.
Jigon na APC a yankin Yarbawa ya ce, shugaba Buhari ya lashe zabe da 70% a yankin Arewa maso Yamma, don haka Tinubu zai fi kawo kuri'u daga yankinsa a zaben 2023.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa:
“Buhari ya kawo 70% daga yankinsa a dukkanin zabe biyu da ya lashe. Za mu kawo 80% ga Asiwaju a yankin Kudu maso Yammaci a zaben 2023."
APC za ta tabuka abin kirki
Hakazalika, ya bayyana tabbacin cewa, jam'iyyar APC za ta yi abin kirki a zaben mai zuwa a yankin Kudu maso Yamma, don haka ya nemi kungiyoyi da dama su marawa muradin Tinubu a zaben na 2023.
Da yake magana a wata ziyara, kodinetan na TAG ya ce Tinubu ne dai jigo mai karfi, kuma tabbas zai yi nasara a zaben, rahoton Guardian.
Adegbola yace:
"Asiwaju haja ce mai kyau, wacce ke da karfin tallata kanta da ma jam'iyyar."
Ya kuma bayyana cewa, tawagar TAG za ta zo da shirye-shiryen matasa don damawa da dalibai da sauran matasa domin hana su komawa jam'iyyun adawa.
Ya kara da cewa:
”Za mu ci gaba da tallata da'awar neman shugabancin Tinubu ba tare da la'akari da addini ko kabila ba nan da 2023.
"Tawagar za ta ci gaba da tallatawa tare da tabbatar da APC ta ci gaba da mulki a 2023."
Wani Bincike Ya Nuna Peter Obi Ya Fi Sauran ’Yan Takarar Shugaban Kasa Karbuwa a Zaben 2023
A wani labarin, idan da yau za a kada kuri'un zaben 2023, akwai yiwuwar Peter Obi na jam'iyyar LP ya lashe zaben, rahoton Premium Times.
Wani kwarkwaryar zaben bincike da ANAP Foundation ta gudanar a wannan watan, ya nemi ra'ayin jama'a kan fitattun 'yan takarar shugaban kasa na APC; Bola Tinubu, PDP; Atiku Abubakar da NNPP; Rabiu Musa Kwankwaso.
Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP ne ya zo na hudu tare da Obi a farko, Tinubu da Atiku kuwa suka yi kunnen doki.
Asali: Legit.ng