Wani Bincike Ya Nuna Peter Obi Ya Fi Sauran ’Yan Takarar Shugaban Kasa Karbuwa a Zaben 2023
- Yayin da zaben 2023 ke kara gabatowa, akwai yiwuwar Peter Obi ya lashe zabe kamar yadda wani bincike ya tabbatar
- An yi binciken da ya gwada karbuwar Atiku, Tinubu, Peter Obi da Kwankwaso, sakamako ya bayyana
- 'Yan siyasa na ci gaba da tallata 'yan takararsu gabanin zaben 2023 mai zuwa, shekarar da Buhari zai yi sallama da Villa
Najeriya - Idan da yau za a kada kuri'un zaben 2023, akwai yiwuwar Peter Obi na jam'iyyar LP ya lashe zaben, rahoton Premium Times.
Wani kwarkwaryar zaben bincike da ANAP Foundation ta gudanar a wannan watan, ya nemi ra'ayin jama'a kan fitattun 'yan takarar shugaban kasa na APC; Bola Tinubu, PDP; Atiku Abubakar da NNPP; Rabiu Musa Kwankwaso.
Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP ne ya zo na hudu tare da Obi a farko, Tinubu da Atiku kuwa suka yi kunnen doki.
Za dai a kada kuri'u a zaben 2023 mai zuwa nan da watan Fabrairun shekarar mai zuwa ga rabon ganin badi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Fashin bakin sakamakon binciken na ANAP Foundation
Sakamakon da aka samu ya nuna cewa Peter Obi yana tasirin 21% na masu kada kuri’a yayin da Bola Tinubu na APC da Atiku Abubakar na PDP suka yi kunnen doki da 13% kowannensu.
A bangare guda, dan takarar NNPP kumatsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya zo da 3% kacal na kur'u.
Sanarwar da mu'assasin ANAP Foundation, Atedo Peterside ta bayyana cewa, akwai wadanda basu zabi dan takara ko daya ba, rahoton Business Day.
Atedo Peterside ya ce, kaso 32% ba su yanke shawarin wadanda za su zaba ba, 15% sun gwammaci boye sunan 'yan takararsu.
Tinubu Ya Samu Gagarumin Goyon Baya Daga Wani Shahararren Malamin Addini, Ya Ce Shine Zai Gyara Najeriya
Gwamna Makinde Ya Tarbi Atiku, Okowa, Mambobin NWC Na PDP, Da Sauran Jiga-Jigai
A wani labarin, The Nation ta ruwaito cewa, Gwamnan Seyi Makinde na jihar Oyo ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar a gidan gwamnatin jihar dake Agodi, birnin Ibadan.
Atiku dira gidan gwamnatin na Oyo ne tare da abokin gaminsa a tafiyar 2023, Ifeanyi Okowa da misalin karfe 11:46 na safe.
Hadimin gwamnan jihar, Bayo Lawal ne ya tarbe su a filin jirgin sama na Ibadan, kamar yadda rahotanni suka bayyana, rahoton BluePrint.
Asali: Legit.ng