2023: Jigon NNPP Ya Yi Hasashen Yadda Za Ta Kare da Atiku, Tinubu, Obi da Kwankwaso
- Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yace zaben shugaban kasan 2023 zai iya zuwa da abin mamaki
- ‘Dan takarar gwamnan na Kaduna yana ganin babu ‘dan takarar da zai samu galaba a tashin farko
- Suleiman Hunkuyi yana ganin dole sai wankin hula ya kai dare ga duk jam’iyyar da za ta ci zabe
Kaduna - ‘Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin NNPP, Suleiman Othman Hunkuyi, yace zaben shugaban kasa na 2023 zai zo nr da sabon salo.
Sanata Suleiman Othman Hunkuyi yace a yadda abubuwa ke tafiya, da alama sai zaben 2023 ya je ga zagaye na biyu, Vanguard ta kawo wannan rahoto.
‘Dan siyasar yake cewa zai yi wahala a samu ‘dan takaran da zai lashe zaben shugabancin Najeriya a karon farko, idan aka yi la’akari da dokar zabe.
A ra’ayin tsohon Sanatan na Arewacin jihar Kaduna, babu wata jam’iyya da za a raina a zaben shekara mai zuwa, domin za a iya ganin abin ban mamaki.
Rahoton The Sun yace Suleiman Hunkuyi ya fadawa manema labarai a ranar Laraba cewa ‘yan takarar shugabancin kasa sun sa batun addini da kabilanci.
A cewar Hunkuyi, samun akalla 25% na kuri’un da aka kada a jihohi 25 zai yi wa ‘yan takara wahala a karon farko, watakila sai an yi zagaye na biyu tukun.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Abin da Suleiman Othman Hunkuyi ya hango
“Alamu na nuna babu wata jam’iyya, har da NNPP da za tayi nasara daga zagayen farko. Watakila sai an je ga zagaye na biyu.
Domin dokar zabe ta bukaci a samu kuri’un da aka kada daga kowane yanki na jihohi, baya ga samun kuri’un da suka fi rinjaye.
“Ina jin cewa babu wata jam’iyya guda, ko ‘dan takara guda da zai iya yin asara, shiyasa doka ta tanadi yin wani zagayen zaben."
- Suleiman Othman Hunkuyi
Jam'iyyar NNPP ta tsorata?
Kamar yadda ya zo a Daily Trust yau da safe, Hunkuyi yana cewa wannan bai nufin yana ganin jam’iyyarsu ta NNPP ba zata je ko ina ba a zaben na badi.
Kwararren ‘dan siyasar yace PDP da APC sun fi kowa karfi, amma idan aka yi nazarin zaben, zai yi wahala a tashin farko suyi nasara a jihohin da ake da su.
Peter Obi ba zai ci zabe ba - FFK
An rahoto Femi Fani-Kayode yana cewa Peter Obi ya sani sarai ba zai ci zabe ba, shiyasa yake neman tada yaki tsakanin Hausawa, Yarbawa da Ibo.
Jigon na APC ya tona wadanda suke tare da ‘Dan takaran na LP, yace babu jihar da Obi da jam’iyyarsa za su iya samun 10% na kuri'un da za a kada a 2023.
Asali: Legit.ng