Abun Kallo Yayin da Wani Gwamnan APC Ya Garkame Kofa Ya Hana Ma'aikata Shiga Gidan Gwamnati

Abun Kallo Yayin da Wani Gwamnan APC Ya Garkame Kofa Ya Hana Ma'aikata Shiga Gidan Gwamnati

  • Abu kamar wasan kwaikwayo yayin da gwamna Ayade ya hana dukkan ma'aikatan da suka zo a makare shiga gidan gwamnati
  • Gwamnan Kuros Ribas ya isa Ofishinsa kafin ƙarfe 8:00 na safe amma bisa mamaki da yawan ma'aikata ba su zo ba
  • Bayanai sun cewa ma'aikata kusan 100 aka bari yashe a wajen bayan kulle babbar Ƙofar shiga wurin ayyukan su

Cross River - An samu wata hatsaniya mai kama da wasan kwaikwayo ranar Laraba da safe sa'ilin da gwamnan jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya bar ma'aikatan gidan gwamnati cirko-cirko a waje.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa gwamnan na jam'iyyar APC ya kulle babbar ƙofar shiga gidan gwamnatin jihar dake Kalaba, ya hana duk wasu ma'aikata da suka makara shiga.

Kara karanta wannan

2023: Dogara Da Babachir Sun Gana Da Kiristocin Arewa Don Kalubantar Gamin Tinubu Da Shettima

Gidan gwamnatin Kuros Riba.
Abun Kallo Yayin da Wani Gwamnan APC Ya Garkame Kofa Ya Hana Ma'aikata Shiga Gidan Gwamnati Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa Ayade ya isa wurin aiki tun kafin ƙarfe 8:00 na safe kuma ya umarci shugaban dakarun tsaro (CSO) ya kulle babbar Ƙofar shiga gidan gwamnati, kada a bar duk wanda ya zo bayan ƙarfe 8:00 ya shiga Ofis.

Yayin da wakilin jaridar ya ziyarci Ofishin gwamna da misalin ƙarfe 10:45 na hantsi ya tarad da ma'aikata kusan 100 sun yi cirko-cirko a ƙofa yayin da wasu suka fara kama gabansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiya da ta nemi a ɓoye bayananta, ta faɗa wa yan jarida cewa gwamnan ya sha mamaki yadda yaga da yawan ma'aikata ba su kama aiki ba lokacin ya isa Ofis.

"Nan take ya ba da umarnin dawo da littafin rijista da lokacin zuwa aiki, sannan ya umarci shugaban jami'an tsaro ya kula da babbar Kofar shigowa ya hana kowane makararren ma'aikaci," inji majiyar.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Shiga Wata Matsala, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Koma Bayan Gwamna Wike

Wane ma'aikata matakin ya shafa?

Bincike ya nuna cewa waɗan da aka bari zaune a waje saboda makara sun haɗa da manya a ɓangaren aiki da Ofisoshi daban-daban da kuma naɗe-naɗen siyasa da suka ƙunshi mashawartan gwamna na musamman.

Da aka tuntuɓe shi mai magana da yawun gwamna Ayade, Christian Ita, yace gwamna ba ya ɗaukar kowane kalan wasa da aiki kuma yana kyautata wa waɗan da ke kokarin sauke haƙƙinsu.

"Kowa ya san ƙarfe 8:00 ne lokacin zuwa wurin aiki kuma idan har gwamna zai kiyaye ya zo a kan lokaci, me zai sa wasu su makara."

A wani labarin kuma Sabuwar Matsala Ga Atiku, Ɗan Takarar Gwamna Ya Fice Daga Jam'iyyar PDP a Arewa

Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Yobe karƙashin PDP ya tsame jikinsa daga harkokin jam'iyyar, ya sanar da yin murabus.

Alhaji Abba Gana Tata, ya sanar da jagororin PDP a jihar Yobe cewa daga ranar 13 ga Satumba, 2022, ya fice daga jam'iyyar baki ɗaya.

Kara karanta wannan

2023: Ana Gab da Fara Yakin Neman Zaɓe, Atiku da PDP Sun Gamu da Gagarumin Cikas a Jihar Arewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel