Atiku Abubakar: Abubuwan da Zan Yi a Kwanaki 100 na Farko da Zan Yi a Ofis
- Atiku Abubakar ya ziyarci jihar Legas, ya yi bayanin manufofinsa a gaban wasu manyan ‘yan kasuwa
- ‘Dan takaran ya yi wa Duniya bayanin yadda zai farfado da tattalin arzikin Najeriya idan ya lashe zabe
- Wazirin Adamawa zai yi kokarin cire tallafin mai, ya rage cin bashi a cikin kwanaki 100 na farko
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Lagos - ‘Dan takarar jam’iyyar PDP na zaben shugaban kasa, Atiku Abubakar yace zai fito da wani asusun Dala biliyan 10 domin ya farfado da tattalin arziki.
A ranar Talata, 13 ga watan Satumba 2022, Daily Trust ta rahoto Alhaji Atiku Abubakar yana bayanin yadda zai fara mulki idan ya zama shugaban kasa.
‘Dan takaran yake cewa a kwanaki 100 na farko da zai yi a kan mulki, zai maida hankali wajen taimakawa matsakaita da kananan ‘yan kasuwan kasar nan.
Rahoton yace Atiku Abubakar ya yi wannan bayani ne wajen gabatar da manufofin tatalin arzikinsa a gaban ‘yan kasuwa a taron da LCCI ta shirya a garin Legas.
A wajen taron Atiku ya sha alwashin tallafawa tsare-tsaren MSME, yace hakan zai farfado da tattalin arziki. A halin yanzu ana fama da matsalar talauci a Najeriya.
Wazirin na Adamawa yace zai dauki matakan da za su canza tsarin kashe kudi, sannan zai yi bakin kokari wajen ganin dukiya na yawo a al’umma a mulkinsa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hanyar da mu za kawo sauyi - Atiku
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi alwashin daukar matakai biyar da suka hada da duba yadda gwamnatin tarayya take kashe kudi da kuma rage facaka.
Idan har Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa a watan Mayun 2023, gwamnati za ta cire tallafin man fetur, kuma zai daina taimakawa kamfanonin cikin gida.
A cikin jawabinsa, Atiku yace zai duba abin da gwamnatin tarayya take batarwa wajen albashi, baya ga haka zai tabbatar an rage cin bashi a wajen yin ayyuka.
Muddin mulki ya koma hannun Atiku, abin da gwamnatinsa za ta rika kashewa wajen biyan albashi da makamantansu ba za su zarce 45% a kasafin kudi ba.
Gwamnatin PDP za ta hada-kai da ‘yan kasuwa wajen yin muhimman ayyukan more rayuwa. The Nation tace sauran sauran ‘yan takara su gabatar da manufofinsu.
Magance matsalar ASUU - Obi
An ji labari Peter Obi mai takarar shugabancin Najeriya a inuwar Labour Party ya sake yin magana a game da yajin-aikin da ‘Yan ASUU suke yi tun Fubrairu.
‘Dan takarar shugaban kasar yace idan aka yi amfani da cinikin danyen man wata daya, an gama magana. Watanni bakwai kenan da daina karatu a jami'o'i.
Asali: Legit.ng