Zan Cire Najeriya Daga Kungurmin Duhu Idan Na Gaji Buhari, Inji Dan Takarar PDP Atiku
- Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP ya bayyana irin halin da Najeriya ke ciki a karkashin mulkin APC
- Dan takarar shugaban kasan na PDP ya ce zai cire Najeriya daga kangi idan aka zabe shi a zaben 2023
- Atiku ya ce Najeriya a dabaibaye take da tarin bashi tun farkon mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Legas - Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin fidda Najeriya Najeriya daga kungurmin duhun da take ciki idan aka zabe shi a zaben 2023.
Ya bayyana haka ne yayin da yake magana a wani taron kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) ta 2022 da aka yi a Legas, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma shawarci 'yan Najeriya da cewa, kada su rudu da siyasar farfaganda da barbade a kafafen Facebook, Twitter da Instagram, inda yace hakan ba zai kare su da komai ba.
Ya ce, ya yi fafutuka da yawa a rayuwa, kuma babu abin da ke bashi farin ciki illa ya ga ya sanya wani ya samu arzikin a zo a gani.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake bayyana kadan daga manufofinsa, ya ce ya shirya tsaf don tabbatarwa da inganta tattalin arzikin Najeriya matukar ya gaji Buhari.
An dabaibaye Najeriya da bashi
A bangare guda, Atiku ya koka da yadda Najeriya ke cikin matsin tattalin arziki, kana ake samun faduwa maimakon tashi a fannin.
Ya ce, daya daga cikin manufofinsa shine inganta kasa ta fannin tattalin arziki, don haka zai yi kokarin cire Najeriya daga kangin.
A cewar Atiku, Najeriya a dabaibaye take da dimbin bashi da tuni ya riga ya yi mata katutu.
Ya kuma shaida cewa, Najeriya a karkashin mulkin APC bata samu wani karuwa ba illa gibin da kullum take samu a kasafin kudi, rahoton Pulse.
Manyan Mambobin PDP Sun Yi Dafifi a Legas, Za Su Karbi Bakuncin Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku
A wani labarin, daruruwan jiga-jigai da mambobin jam'iyyar PDP ne suka mamaye filin jirgin saman Muritala Mohammed dake Legas domin karbar dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Kamfanin dillacin labarai na Najeriya ya ce, magoyta bayan Atiku sun taru a filin jirgin ne tun misalin karfe 7 na safiyar yau Talata, 13 ga watan Satumba, The Guardian ta ruwaito.
Ya zuwa karfe 1 na rana, rahoton ya ce Atiku Abubakar bai dira filin jirgin ba tukuna.
Asali: Legit.ng