Manyan Mambobin PDP Sun Yi Dafifi a Legas, Za Su Karbi Bakuncin Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku

Manyan Mambobin PDP Sun Yi Dafifi a Legas, Za Su Karbi Bakuncin Dan Takarar Shugaban Kasa Atiku

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP zai kai wani ziyara jihar Legas don halartar wasu taruka
  • Jiga-jigai da mambobin jam'iyyar PDP da dama sun taru domin tarbar dan takara Atiku Abubakar
  • 'Yan siyasa a Najeriya na ci gaba da yawon neman goyon baya daga fannoni daban-daban a a kasar nan

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Legas - Daruruwan jiga-jigai da mambobin jam'iyyar PDP ne suka mamaye filin jirgin saman Muritala Mohammed dake Legas domin karbar dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar.

Kamfanin dillacin labarai na Najeriya ya ce, magoyta bayan Atiku sun taru a filin jirgin ne tun misalin karfe 7 na safiyar yau Talata, 13 ga watan Satumba, The Guardian ta ruwaito.

Ya zuwa karfe 1 na rana, rahoton ya ce Atiku Abubakar bai dira filin jirgin ba tukuna.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya lallaba, ya yi ganawar sirri da dan takarar shugaban kasan AA, Al-Mustapha

Shugabannin PDP a Legas sun taru, za su karbi a Atiku
Manyan mambobin PDP sun yi dafifi a Legas, sun karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa Atiku | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Mr Hakeem Amode kakakin PDP a Legas ya ce, jam'iyyar ta tattara kadan daga jiga-jigai da mambobinta ne domin karbar dan takarar.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa, ilahirin mambobin PDP a jihar ta Legas na farin cikin karbar Atiku Abubakar.

Abin da zai kai Atiku Legas

An ruwaito cewa, Abubakar zai halarci wani taro ne na kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu ta Legas (LCCI) na shekarar 2022.

Hakazalika, zai halarci taron kungiyar Editocin Najeriya da zai tattauna batutuwa da suka shafi zaben 2023 mai zuwa, rahoton EagleOnline.

'Yan takarar shugaban kasa a Najeriya a zaben 2023 na ci gaba da yawon neman goyon baya da tarukan bayyana manufofinsu a fadin kasar nan.

Yadda Mambobin APC 5,000 Suka Sauya Sheka Zuwa PDP a Jihar Kwara

A wani labarin, an samu tsaiko a APC yayin da dubban mambobinta a Ilorin ta jihar Kwara suka bayyana sauya sheka zuwa PDP.

Kara karanta wannan

Yanzun nan: PDP ta fadi matsayar ta kan ko Ayu zai ci gaba da kasancewa shugabanta

Jaridar Thisday ta ruwaito cewa mambobin na jam’iyyar APC wadanda aka ce ba su gaza 5,000 ba sun saki jam'iyyar su Buhari kuma mai mulki a jihar zuwa ta adawa.

An tattaro cewa, wadannan jiga-jigai na APC da suka hakura suka koma PDP sun fito ne daga unguwanni da kananan hukumomin jihar Kwara da suka hada da Ilorin ta Yamma da kuma karamar hukumar Asa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel