2023: Goyon Bayan Jam'iyyar PDP a Jihar Katsina 'Jihadi' Ne, Lado Ɗanmarke
- Ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a inuwar jam'iyyar PDP yace zaɓen jam'iyyarsa a 2023 ya zama Jihadi
- Da yake jawabi bayan karɓan tubar dubbanin mambobin jam'iyyu da suka koma PDP, yace ga dukkan alamu zai lashe zaɓen jihar
- Dadanzon mambobin jam'iyyun siyasa har da PDP a ƙaramar hukumar Safana sun sauya sheka zuwa PDP
Katsina - Yakubu Lado Ɗanmarke, mai neman kujerar gwamnan jihar Katsina a 2023 karkashin inuwar PDP yace mara wa jam'iyyarsa baya har ta lashe zaɓe ya zarce a kira shi siyasa kawai.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito ɗan takarar gwamnan a jihar da Buhari ya fito na cewa, "Jihadi Ne" goyon bayan PDP da kuma dangwala mata ta lashe zaɓen Katsina.
Lado ya yi wannan furucin ne yayin zantawa da yan jarida a Katsina bayan karɓan tuban dandazon mambobin jam'iyyu da dama har da APC waɗanda suka koma PDP a ƙaramar hukumar Safana.
Ya nuna kwarin guiwar cewa bisa la'akari da yadda mutane ke tururuwar sauya sheka a jihar, alama ce ta lokaci kawai ake jira a ayyana shi zaɓaɓɓen gwamna da tazara mai nisa.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
PDP a Katsina tana zaune lafiya - Lado
"A nan jihar Katsina, jam'iyyar PDP na zaune lafiya babu rarrabuwar kai a cikinta. Na fafata da yan takara uku a zaɓen fidda gwani, amma a halin yanzu muna tare da juna."
"Ɗaya daga cikinsu ne ya zama abokin takarana (ɗan takarar mataimakin gwamna) sannan kuma ɗayan zai nemi kujerar ɗan majalisar tarayya."
"Na ƙarshe kuma a koda yaushe yana tare da mu kuma duk abinda muka sanya a gaba muna zuwa neman shawarinsa, yana bamu shawarwari masu kyau da daraja."
- Lado Ɗanmarke.
A wani labarin kuma kun ji cewa Atiku Ya Rubuta Wasika Ta Musamman Ga Yan Najeriya, Ya Faɗi Zaɓi Biyu Da Ya Rage Wa Mutane a 2023
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ankarar da yan Najeriya kan zaɓi biyu da suke da shi a 2023.
Atiku, mai neman kujerar shugaban kasa a inuwar PDP, yace 'yan Najeriya zasu tantance tsakanin yanci da azaba.
Asali: Legit.ng