An Kai Korafi Zuwa Hedikwata, Ana Zargin Shugabannin APC da Satar Miliyoyin Kudi

An Kai Korafi Zuwa Hedikwata, Ana Zargin Shugabannin APC da Satar Miliyoyin Kudi

  • Wasu ‘ya ‘yan APC sun rubuta takardar korafi, suna zargin an saci miliyoyin kudi a asusun jam’iyya
  • Idowu Olaonipekun da Ayinde Suuru daga APC ta reshen jihar Ogun sun ce an sulale da akalla N74m
  • Masu korafin sun kai kara ne wajen Shugaban APC na kasa, Abdullahi Adamu, dauke da bayanai

Abuja - Wasu daga cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na reshen jihar Ogun sun kai korafi gaban shugaban jam’iyyan suna zargin shugabanninsu da sata.

Premium Times ta kawo rahoto a ranar Asabar cewa wadannan ‘yan jam’iyya sun fadawa Abdullahi Adamu an saci kudi daga asusun jam’iyya a Ogun.

Idowu Olaonipekun daga mazabar Owode a karamar hukumar Yewa ta kudu da Ayinde Suuru daga mazabar Ifohintedo da ke Ipokia suka shigar da karar.

Kara karanta wannan

Atiku da Danmarke Sun Kwashewa Tinubu da Kwankwaso Mabiya 13, 000 a Katsina

Masu korafin sun ce shugaban APC na reshen Ogun, Yemi Sanusi, da sakatarensa watau Aderibigbe Tella sun dauke akalla N74m, sun zuba a aljihunsu.

Magana ta je gaban NWC

Olanipekun da Suuru sun sanar da Sanata Abdullahi Adamu cewa sun kawo maganar a gabansa ne bayan sun bankado takardun bankin da aka yi aika-aikar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton yace an shigar da korafin ne a ranar 7 ga watan Satumba 2022 dauke da bayanin yadda sakataren APC na jiha ya tura kudi zuwa ga shugaban jam’iyya.

Shugaban APC
An kai zuwa wajen Shugaban APC Hoto: @OfficialAPCNig
Asali: UGC

Ana zargin sakataren na APC da tura kudi daga asusun jam’iyya zuwa wani akawun na sakataren gudanarwa na jam’iyya, an bada lambabobin akawun din.

Me za ayi da wannan kudi?

A cewar masu karar, an dauke wadannan kudi tsakanin Afrilu zuwa Agustan shekarar 2021, duk da cewa jam’iyyar ba ta da dawainiyar da za ta bukaci kudin.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

‘Ya ‘yan jam’iyyar sun ce babu dalilin da jam’iyya za ta kashe wadannan miliyoyi domin Gwamna Dapo Abiodun yake daukar duk nauyin APC da N7m duk wata.

Takardar ta kara da cewa shugabannin reshen jihar ba su taba fitar da kudi na ayyuka a kananan hukumomi ko mazabu ba, sai yanzu suka buge da gyaran ofis.

APC ta samu labari

Kakakin APC, Tunde Oladunjoye, ya tabbatar da cewa an kai wannan korafi, yace ba aikin kowa ba ne sai wasu ‘yan taware da ba jam’iyya ta yanke masu cibiya ba.

A wannan takarda, an ankarar da jagoran APC na reshen Ogun, Segun Osoba; tsohon gwamna, Ibikunle Amosun; sai Sanataoci; Tolu Odebiyi da Lekan Mustapha.

Umahi ya yabi Obidients

A makon jiya aka ji Gwamna David Umahi yace Jam’iyyar LP da Peter Obi suna kara farin jini sosai a Kudancin kasar nan, amma bai isa ayi nasara a kan APC ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Soke Zaben Fidda Gwanin Jam'iyyar APC Biyu a Arewa

Gwamnan ya yabawa tafiyar Peter Obi, yace hakan zai iya yin sanadiyyar da nan gaba Mutumin Ibo zai zama shugaban kasa bayan lokaci ana jiran tsammani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng