Gwamna Makinde Ya Maye Gurbin Tambuwal a Kujerar Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP

Gwamna Makinde Ya Maye Gurbin Tambuwal a Kujerar Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP

  • Jam'iyyar PDP ta yi zaman warware matsalolin da suka mamaye ta, an yi sauye-sauye da dama
  • Gwamnan jihar Sokoto ya sauka daga kujerar shugabantan kungiyar gwamnonin jam'iyyar ta PDP
  • An nada gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo a matsayin sabon shugaban kungiyar gwamnonin PDP

FCT, Abuja - Jim kadan bayan da gwamnan jihar Sokoto Tambuwal ya sauka daga mukamin shugaban gwamnonin PDP, an sanar da gwamna Seyi Makinde a matsayin wanda ya maye gurbinsa.

Gwamnan Oyo ya zama sabon shugaban gwamnonin PDP ne a yau Alhamis 8 ga watan Satumba a taron majalisar zartaswar PDP dake gudana a Abuja.

Makinde ya maye gurbin Tambuwal a shugabancin gwamnonin PDP
Gwamna Makinde Ya Maye Gurbin Tambuwal a Kujerar Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP | Hoto: thedefenderngr.com
Asali: UGC

An bayyana Makinde a matsayin sabon shugaban kungiyar ne mintuna kadan bayan da Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana yin murabus, rahoton 21st Century Chronicle.

A yau ne ake dinke barakar da ta shafi shugabancin jam'iyyar PDP, kujeru da dama sun samu sabbin shugabannin bayan cire wasu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Mun Gano Kayan Sojoji, Makudan Kudade A Gidan Tukur Mamu, DSS

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam'iyyar PDP na cikin rikici tun bayan da aka kammala zaben fidda gwani.

Bayan Shugaban BoT Ya Yi Murabus, Kujerar Gwamna Tambuwal Ta Fara Tangal-Tangal a PDP

Shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi murabus daga kujerarsa, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Aminu Tambuwal, gwamnan jihar Sakkwato daga arewacin Najeriya, ya sanar da murabus ɗinsa ne a wurin taron kwamitin amintattu (BoT) dake gudana yanzu haka a Abuja.

Tun farko, Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa shugaban BoT na ƙasa, Sanata Walid Jibrin, ya sauka daga kan muƙaminsa, lamarin da ya jefa kujerar Tambuwal cikin rashin tabbas

Majalisar Zartaswar Jami’iyyar PDP Ta Amince Ayu Ya Ci Gaba da Shugabantar Jam’iyya

A wani labarin, wani rahoton Punch ya ce, majalisar zartaswar jam’iyyar PDP ta kasa ta amince Sanata Iyorchia Ayu ya ci gaba da shugabancin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Aminu Tambuwal Ya Yi Murabus Daga Kan Muƙaminsa Na PDP

Wannan na zuwa ne bayan majalisar ta NEC ta kada kuri'ar amince da Ayu, wanda hakan ke nufin shugaban jam’iyyar ba zai sauka daga mukaminsa a nan kusa ba.

Ana ci gaba da kai ruwa rana a jam'iyyar PDP game da shugabancin jam'iyyar, tun bayan barkewa rikici tsakanin gwamnan Ribas Wike da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel