Majalisar Zartaswar Jami’iyyar PDP Ta Amince Ayu Ya Ci Gaba da Shugabantar Jam’iyya

Majalisar Zartaswar Jami’iyyar PDP Ta Amince Ayu Ya Ci Gaba da Shugabantar Jam’iyya

  • A yau ne jam'iyyar PDP ta tashi da kokarin warware duk wata baraka dake tattare da ita gabanin fara kamfen
  • An samu rashin jituwa tsakanin dan takarar shugaban kasa na PDP da gwamnan jihar Ribas a PDP
  • Majalisar NEC ta PDP ta amince sanata Ayu ya ci gaba da shugabantar jam'iyyar, babu shirin sauke shi nan kusa

FCT, Abuja - Wani rahoton Punch ya ce, majalisar zartaswar jam’iyyar PDP ta kasa ta amince Sanata Iyorchia Ayu ya ci gaba da shugabancin jam'iyyar.

Wannan na zuwa ne bayan majalisar ta NEC ta kada kuri'ar amince da Ayu, wanda hakan ke nufin shugaban jam’iyyar ba zai sauka daga mukaminsa a nan kusa ba.

Majalisar zartaswar PDP ta amince Ayu ya ci gaba da mulkar jam'iyya
Majalisar zartaswar jami'iyyar PDP Ta amince Ayu ya ci gaba da shugabantar jam'iyya | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ana ci gaba da kai ruwa rana a jam'iyyar PDP game da shugabancin jam'iyyar, tun bayan barkewa rikici tsakanin gwamnan Ribas Wike da dan takarar shugaban kasa na PDP Atiku.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamna Aminu Tambuwal Ya Yi Murabus Daga Kan Muƙaminsa Na PDP

Idan baku manta ba, an samu kiraye-kiraye daga mambobin jam'iyyar PDP kan cewa, ya kamata Ayu ya hakura ya ajiye mukaminsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin Atiku

Kafar labarai ta Channels Tv ta ce, Atiku Abubakar ya yi tsokaci game da rikice-rikicen da jam'iyyar PDP ke fuskanta, inda yace ana kokarin warware komai.

A cewarsa, ba sabon abu bane a samu rikici a kowane ahali, kuma daga baya a samu warwarewar komai a koma daidai.

Hakazalika, Atiku ya kuma bayyana cewa, jam'iyyar PDP na kundin tsarin mulki dake taimakawa mambobi wajen tafiyar da al'amaranta.

Har yanzu dai ana ci gaba da jiran abubuwan da za su fito daga jam'iyyar ta PDP.

Majalisar Dokokin Jihar Neja Ta Tsige Shugaban Masu Rinjaye da Mataimakiyarsa

A wani labarin, a yau Alhamis 8 ga watan Satumba muke samun labarin cewa, 'yan majalisar dokokin jihar Neja sun karbe kujerar shugaban masu rinjaye, mataimakinsa da kuma shugaban masu tsawatarwa na majalisa.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Gini Mai Hawa 4 Ya Rushe Ya Fada Kan Mutane Da Dama A Ibadan

Rahoton ya kuma bayyana cewa, tuni 'yan majalisar suka zabo wadanda za su gaje su nan take, The Nation ta ruwaito.

Jami'an majalisar da aka tsige sune shugaban masu rinjaye Saleh Ibrahim, mataimakiyarsa Binta Mamman da shugaban masu tsawatarwa na majalisa Bello Ahmed.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.