Yadda Tinubu, Kwankwaso da Obi Suka Goyi Bayan Atiku ya Zama Shugaban Kasa

Yadda Tinubu, Kwankwaso da Obi Suka Goyi Bayan Atiku ya Zama Shugaban Kasa

  • Atiku Abubakar ya dade yana neman zama shugaban Najeriya, wannan ne karo na shida yake yin takara
  • ‘Dan takaran shugaban kasar na PDP ya tabe shiga zabe a karkashin jam’iyyun ACN da PDP a 2011 da 2019
  • An yi lokutan da Bola Tinubu, Rabiu Kwankwaso da Peter Obi suka goyi bayan Atiku ya dare kan mulki

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

A wannan rahoto na musamman da muka fitar, mun kawo lokutan da manyan ‘Yan takaran shugabancin Najeriya suka marawa Atiku Abubakar baya.

1. Zaben 2003

A zaben shugaban kasa na 2003, Rabiu Musa Kwankwaso ya goyi bayan Atiku Abubakar da Olusegun Obasanjo su zarce, su koma kan karagar mulki.

Ko da Atiku Abubakar bai yi takarar shugaban kasa ba, shi ne mataimakin shugaban Najeriya. Kwankwaso a lokacin yana gwamna ya goyi bayan PDP.

Kara karanta wannan

2023: Lokaci Ya Yi Da Arewa Zata Saka Wa Bola Tinubu, Shettima

2. Zaben 2007

Zuwa 2007, Atiku Abubakar ya yi baram-baram da Olusegun Obasanjo, a lokacin Bola Tinubu ya taimaka wajen ba shi takarar shugaban kasa a jam’iyyar AC.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Duk da goyon bayan da Bola Tinubu ya ba Atiku, jam’iyyar AC ba ta iya doke Umaru ‘Yar’adua ba. Daga baya tsohon mataimakin shugaban kasar ya dawo PDP.

Atiku
Atiku Abubakar a taron siyasa Hoto: @Atiku.org
Asali: Facebook

3. Zaben 2011

Ana tunanin Rabiu Kwankwaso ya goyi bayan Atiku Abubakar ya zama ‘dan takaran shugaban kasa a PDP a zaben 2011, amma Goodluck Jonathan ya samu tikiti.

A karshe shugaban kasa mai-ci Goodluck Jonathan ya yi nasara a kan CPC, ACN da irinsu ANPP.

4. Zaben 2019

Atiku Abubakar ya doke su Rabiu Kwankwaso wajen samun takara a PDP a 2019, Sanatan na Kano yana cikin wadanda suka goyi bayan ya karbi mulkin kasa.

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Na Da Ɗan Takara? Tsohon Shugaban Kasar Ya Bada Amsa

A wannan zabe ne Atiku ya dauko Peter Obi a matsayin abokin takara, Obi ya bada gudumuwa sosai a wajen takaran, wannan bai sa sun yi doke APC ba.

Za a dama da matasa a 2023?

A jiya aka ji Bola Ahmed Tinubu da Sanata Kashim Shattima sun sha alwashin ba wa mata sama da kaso 35 cikin 100, shi ma Atiku ya yi irin wannan alkawari.

Aminu Gadagau wanda ya nemi takarar ‘dan majalisa a Giwa, jihar Kaduna ya shaida mana Bola Tinubu zai tafi da matasa idan ya ci zaben shugaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel