2023: Abin Da Yasa Na Ki Shiga APC Da PDP, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP

2023: Abin Da Yasa Na Ki Shiga APC Da PDP, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP

  • Farfesa Christopher Imumolen, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar AP ya bayyana dalilan da yasa bai shiga APC ko PDP ba
  • Imumolen ya ce ya yi nazari ya gano cewa jam'iyyun biyu sun gaza samarwar yan Najeriya romon demokradiyya tun shekarar 1999
  • A cewarsa, hakan na nufin tsarin jam'iyyun biyu ba zai taba kawo hanyar warware matsalolin kasar ba don haka akwai bukatar nemo sabbin hanyoyi

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Accord Party, (AP), Farfesa Christopher Imumolen, ya ce ya ki shiga APC da PDP ne saboda 'gazawarsu' na shekaru a kasar.

Ya ce ya yanke shawarar shiga jam'iyyar Accord ne bayan yin nazari kan APC da PDP, wadanda ya yi ikirarin sun gaza samarwa yan Najeriya romon demokradiyya.

Imumolen
Abin Da Yasa Na Ki Shiga APC Da PDP, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

2023: Najeriya Ba Za Ta Zauna Lafiya Ba Idan Mulki Ya Tsaya A Arewa, In Ji PANDEF

A cewarsa, ban shiga APC da PDP ba saboda bukatar kauracewa tsarin da ya gaza samarwa yan Najeriiya romon demokradiyya kimanin shekaru 20 bayan dawowa mulkin demokradiyya.

Imumolen ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a kungiyar yakin neman zabensa ta bawa The Punch a ranar Laraba.

Wani bangare na sanarwar:

"Na yanke shawara ba zan shiga jam'iyyun da ake kira manya ba saboda ina son sabon tsarin gwamnati ne.
"Na fada wa kai na cewa idan har canji na ke son kawowa da gaske, ya kamata in nesanta kaina daga tsarin da ya gaza yi wa yan Najeriya aiki duk da irin masu ilimi da suka yi aiki a cikinsa."

Ya bayyana Najeriya a matsayin kamfani da ke da matsalar kulawa duk da kokarin da ma'aikata suka yi ta yi na kawo canji.

Don haka ya ce akwai bukatar wani daga waje wanda matsalolin kamfanin ba su shafe shi ba ya taho ya kawo sabuwar tunani da za a iya gyara kamfanin.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Yasa Peter Obi Ba Zai Iya Cin Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Ba: Jigon APC Ya Yi Magana Mai Karfi

Abin Da Muka Tattauna Da Obasanjo, Dan Takarar Shugaban Kasa Na AP

A bangare guda, Farfesa Christopher Imumolen ya bayyana abin da suka tattauna da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Vanguard ta rahoto cewa ba wannan bane karo na farko da mai fatan zama shugaban kasar ya ziyarci tsohon shugaban kasar.

Yayin ziyarar, hotuna sun nuna farfesan ya rusuna kan gwiwansa yayin da Obasanjo ke masa addu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164