Dalilin Da Yasa Peter Obi Ba Zai Iya Cin Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Ba: Jigon APC Ya Yi Magana Mai Karfi

Dalilin Da Yasa Peter Obi Ba Zai Iya Cin Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Ba: Jigon APC Ya Yi Magana Mai Karfi

  • Dalilin Da Yasa Peter Obi Ba Zai Iya Cin Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Ba: Jigon APC Ya Yi Magana Mai Karfi
  • Bisa alamu dai sunan Peter Obi ta kama bakunan yan Najeriya, amma Patrick Obahiagbon baya tunanin zai iya cin zaben shugaban kasa na 2023
  • A cewar tsohon dan majalisar, dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour Party ba zai iya cin kashi 25 cikin 100 na kuri'u a jihohi 24 ba

Obahiagbon ya bayyana magoya bayan Peter Obi a matsayin yan Najeriya da suka gaji da yan siyasa na yanzu kuma suke son wani sabon abu.

Jigon na jam'iyyar APC ya ce matasan Najeriya sun fara nuna rashin gamsuwarsa da abubuwan da ke faruwa a kasar ne a zanga-zangar EndSARS.

Kara karanta wannan

2023: "Ina Son Abin Da Obi Ke Yi, Zan Gayyace Shi Jiha Ta", In Ji Fitaccen Gwamnan APC

Obi, Atiku da Tinubu
Dalilin Da Yasa Peter Obi Ba Zai Iya Cin Zaben Shugaban Kasa Na 2023 Ba: Jigon APC Ya Yi Magana Mai Karfi. @PeterObi, @atiku @OfficialBAT.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Patrick Obahiagbon, tsohon dan majalisa na wakilai na tarayya, ya ce ya yi imanin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, ba zai iya cin zaben shugaban kasa na 2023 ba.

Tsohon dan majalisar yayin hirar da aka yi da shi a shirin The Morning Show a Arise Television ya ce jam'iyyun APC da PDP ne manyan jam'iyyun da za su fafata a zabe.

Amma, jigon na APC ya bayyana cewa duk da cewa manyan jam'iyyun siyasa biyu na kasar ne za su fafata a zaben, akwai manyan takarar shugabn kasa uku, suna Bola Tinubu (APC), Atiku Abubakar (PDP) da Peter Obi (LP).

Obahiagbon ya ce:

"Ban ga yadda za a yi Labour Party za ta iya samun kashi 25 cikin 100 a jihohi 24 a wannan zaben ba."

Kara karanta wannan

2023: Akwai Ƙulalliya Tsakanin Atiku Da Ayu, Shi Yasa Ya Ƙi Murabus, In Ji Adoke

Su wanene magoya bayan Peter Obi?

Obahiagbon ya ce wadanda ke goyon bayan takarar shugabancin kasa na Obi yan Najeriya ne da suka gaji da yan siyasa na zuwa, The Cable ta rahoto.

Ya bayyana tafiyar ta 'Obidient' a matsayin 'sabuwar tafiya

Tsohon dan majalisar ya ce tafiyar ta Peter Obi na da alaka da rashin gamsuwar da matasa suka yi da abubuwa a kasar kamar yadda suka nuna yayin zanga-zangar ENDSARS a 2020.

Ya yi tambaya:

"Shin Peter Obi zai iya amfani da fushin da yan Najeriya suka yi ta yan siyasan yanzu ya shiga Aso Rock? Ina ganin ba zai yi wu ba. Bana ganin hakan zai yi wu."

Obahiagbon ya ce yana fatan yan siyasan Najeriya za su koyi darasi daga abin da ya janyo matasa suke goyon Peter Obi.

2023: Peter Obi Zai Rasa Takarsa Na Shugaban Kasa A Labour Party? Sabbin Bayanai Sun Fito Fili

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Na Da Ɗan Takara? Tsohon Shugaban Kasar Ya Bada Amsa

A wani rahoton, kun ji cewa tikitin takarar shugaban kasa na Peter Obi a jam'iyyar Labour Party a halin yanzu yana fuskantar barazana bayan rikici da ke faruwa a jam'iyyar a Legas.

Wani rahoto na jaridar Punch ta tabbatar da rikicin da ke faruwa kan jagorancin jam'iyyar a Legas kuma hakan na iya shafar sahihancin dan takarar shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel