Atiku Ya Nada Sabon Mukami, Ya Kawo Wanda Zai Taya Shi Lashe Zaben Shugaban Kasa
- Paul Ibe ya sanar da cewa Alhaji Atiku Abubakar ya sake dauko wanda zai rika magana a madadin kwamitin neman zabe
- ‘Dan takaran na shugaban kasa a jam’iyyar APC ya dauko Charles Aniagwu ya taimakawa Dino Melaye da Daniel Bwala
- Charles Aniagwu kwararren ‘dan jarida ne wanda ya san kan aiki, yayi shekara da shekaru yana wannan harka a jihar Delta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - ‘Dan takarar kujerar shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bada sanarwar nadin mukami a kwamitin kamfe.
Business Day ta kawo rahoto cewa Charles Aniagwu ya zama Kakakin kwamitin yakin neman takarar Alhaji Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP.
A ranar Talata, 6 ga watan Satumba 2022 aka samu labari Mista Aniagwu ya shiga cikin wadanda za su rika magana da yawun kwamitin zaben.
Atiku Abubakar ya bada wannan sanarwa ne a wani jawabi da ya fito daga bakin Paul Ibe.
Ibe yace Aniagwu zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba, zai bada gudumuwa wajen sanar da al’umma game da yakin neman zaben Atiku a 2023.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Aniagwu ya san kan aiki”
“Charles Aniagwu kwararren ‘dan jarida ne wanda ya shafe fiye da shekaru 20 yana aiki a kafofin yada labarai.
“Za iyi aiki tare da sauran wadanda aka bada sanarwar su ne masu magana da yawun bakin kwamitin kamfe”
- Paul Ibe
Da wannan sanarwa, ‘dan jaridar zai yi aiki tare da Sanata Dino Melaye da Daniel Bwala, wadanda zuwa yanzu sune ke magana da yawun kwamitin.
Asali Daniel Bwala Lauya ne, shi kuwa Dino Melaya yayi digir ne a ilmin kasa.
Mutumin Gwamna Ifeanyi Okowa
Yanzu haka Charles Aniagwu shi ne Kwamishinan harkokin yada labarai a jihar Delta. Idan ba a manta ba, daga Delta Atiku ya dauko abokin takara.
Gwamna Ifeanyi Okowa ne ya nada Aniagwu a matsayin kwamishinan labarai, kafin nan ya rike masa kujerar babban sakataren Gwamna a jihar Delta.
Likitoci sun bi LP a 2023
Dazu kun ji labari shugaban kungiyar Docs and Medics for Peter Obi ya yi bayanin dabarar da za a bi domin kai Jam’iyyar Labour Party ga nasara a 2023.
Uche Uzoukwu yace sun fara ratsa lunguna da sako, ana karkato da ra’ayin marasa lafiya domin su zabi Peter Obi, kuma a kawo masa kuri’a miliyan 25.
Asali: Legit.ng