Wike: Babu Wanda Zai Iya Siya Na, Bana Kwadayin Mukamin Gwamnati

Wike: Babu Wanda Zai Iya Siya Na, Bana Kwadayin Mukamin Gwamnati

  • Nyesom Wike, gwamnan Jihar Rivers ya ce babu wani dan siyasa da zai iya siyansa game da babban zaben shekarar 2023
  • Jigon na jam'iyyar PDP ya ce tun shekarar 1999, gwamnatin tarayya karkashin PDP da APC ba ta taba yin wani aiki a jiharsa ba
  • Gwamnan ya ce dole salo zai canja yanzu, yana mai cewa dole sai an fada masa abin da za a yi wa jiharsa kafin su goyi bayan yan takarar shugaban kasa

Rivers - Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers ya ce babu wani dan siyasa da zai iya siyasansa game da babban zaben shekarar 2023, yana mai cewa baya son wani mukami a gwamnatin tarayya, rahoton Daily Trust.

Wike, wanda ya dade yana takun-saka da shugabannin jam'iyyar na PDP, ya ce tun shekarar 1999 goyon bayan da ya ke bawa PDP bai taba sauyawa ba.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Ya Tona Abin da Ya Sa Buhari ya Zarce, Aka Doke Atiku a zaben 2019

Nyesom Wike
Wike: Babu Wanda Zai Iya Siya Na, Bana Kwadayin Mukamin Gwamnati. Hoto: @NewsWireNGR.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tun 1999, Gwamnatin Tarayya Bata Tsinanawa Rivers Komai Ba

Amma, ya ce bai taba amfana da wani aiki na gwamnatin tarayya ba a lokacin mulkin PDP da ma gwamnatin APC mai ci yanzu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar da matsugunin Jami'ar Rivers ta Etche da ke jihar, yana mai cewa ba za a cigaba a haka ba.

Kalamansa:

"Tun 1999, wace jiha ta fi Rivers bawa PDP gudun mawa? Ina kallubalantar duk wata jiha game da goyon bayan PDP. Tun 1999, nuna min aikin gwamnatin tarayya a Jihar Rivers. Akwai ko guda daya? Idan kana son kuri'un mu, fada min abin da za ka yi wa Jihar Rivers.
"Amfani da Jihar Rivers da ake ya isa haka, suna tunanin bamu da wayyo ko bamu san abin da za mu yi da kudi ba. Hankali na yana jiha ta ne. Babu wanda zai iya siya na; ba zan tafi neman mukami a gwamnatin tarayya ba. Ban taba yin minista bane a baya? Don haka mene za ka yi ja hankali na da shi? Babu; ni yanzu abin da zai amfani jiha na nake so."

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Zan Lallasa Tare da Mitsike Kananan Yara, Gwamna Wike

Wike: Sule Lamido Da Abokansa Ne Suka Kayar Da PDP A Zaben 2015

A wani rahoton, Nyesom Wike ya yi shagube ga tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, yana mai cewa ba shi da wata tasiri a siyasar yanzu, The Punch ta rahoto.

Lamido yayin da ya ke magana a shirin Politics Today na Channels Television a daren ranar Talata ya ce babu bukatar yin sulhu tsakanin Wike da Atiku Abubakar domin babu wanda ya yi wa gwamnan na Rivers laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164