'Yan Najeriyan Dake Son Cigaba da Shan Wahala Ne Kaɗai Zasu Zabi APC a 2023, Abdullahi

'Yan Najeriyan Dake Son Cigaba da Shan Wahala Ne Kaɗai Zasu Zabi APC a 2023, Abdullahi

  • Tsohon ministan wasanni a Najeriya kuma ɗan takarar Sanatan Kwara ta tsakiya yace ba ɗan Najeriyan da zai zaɓi APC a 2023
  • Mallam Bolaji Abdullahi, mai neman sanata a inuwar PDP, ya ce wahalallu masu son cigaba da wahala ne zasu yi tunanin ƙara amince wa APC
  • Jam'iyyar PDP da ɗan takararta na shugaban kasa na cikin sahun gaba a waɗan da ake hasashen zasu iya samun nasara a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kwara - Tsohon Ministan wasanni, Mallam Bolaji Abdullahi, yace yan Najeriya dake kaunar cigaba da zama cikin wahalhalu ne kaɗai zasu dangwala wa APC a babban zaɓen dake tafe.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa tsohon Ministan, mai neman kujerar Sanatan shiyyar jihar Kwara ta tsakiya karkashin inuwar PDP, ya yi wannan furucin ne yayin hira da manema labarai a Ilorin.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Buhari Tace Ta Magance Mafi Munin Matsalar Tsaro a Najeriya

Tsohon ministan wasanni, Mallam Bolaji Abdullahi.
'Yan Najeriyan Dake Son Cigaba da Shan Wahala Ne Kaɗai Zasu Zabi APC a 2023, Abdullahi Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

A cewarsa, jam'iyyar APC ta gaza a kowane ɓangaren cigaba kuma ya rataya a wuyan 'yan Najeriya su yi takatsantsan kar su tafka kuskuren maida jam'iyyar kan madafun iko a kowane mataki.

A kalamansa, tsohon ministan yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Sai wanda ke kaunar cigaba da zama cikin wahala ne zai duba yuwuwar dangwala wa jam'iyyar APC bayan kowa na ganin yadda suka lalata ƙasar nan."
"Ba dan ma haka abubuwa suke tafiya ba, bana tsammanin za'a samu wanda zai sake magana game da APC bayan waɗan nan tulin matsalolin da suka kawo a ƙasar nan."
"Babban zaɓe mai zuwa zai kasance na babbar jam'iyyar adawa PDP ne da sauran jam'iyyun siyasar ƙasar nan in banda APC."

Tsohon Ministan ya yi alƙawarin ɗora wa daga inda magabatansa suka tsaya idan ya samu nasarar shiga majalisar dattawa domin haɓaka ɓangaren doka da tabbatar da an ware wa kowane ayyuka isassun kuɗaɗe.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Atiku Abubakar da Gwamna Wike Sun Amince da Bukata Ɗaya Kafin Fara Kamfen 2023

A wani labarin kuma Bayan Shan Kaye, Gwamnan APC Ya Amince da Ɗaukar Sabbin Ma'aikata, Lamarin Ya Tada Ƙura

Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, ya amince da ƙara ɗaukar sabbin malamai dubu ɗaya da ɗari biyar a sassan jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai, Funke Egbemode, yace matakin ɗaukar malaman zai cike gurbin dake tsakanin Malamai da ɗalibai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel