"Na San Tinubu Sama Da Shekaru 50, Amma Ba Zan Iya Goyon Bayansa Ba", Tsohon Minista Mai Goyon Bayan Atiku

"Na San Tinubu Sama Da Shekaru 50, Amma Ba Zan Iya Goyon Bayansa Ba", Tsohon Minista Mai Goyon Bayan Atiku

  • Ebenezer Babatope, tsohon ministan sufuri, ya ce ba zai iya goyon bayan dan takarar shugaban kasa na APC ba saboda ba jam'iyyarsu daya ba
  • Tsohon ministan ya ce duk da cewa ya san tsohon gwamnan na Jihar Legas fiye da shekaru 50, shi (Tinubun) dan APC ne yayin da shi kuma yana PDP ne
  • Babatope ya kuma yi watsi da batun zaben dan takarar shugaban kasar na APC don dukkansu yarbawa ne, ya ce hakan ba za ta yi wu ba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Tsohon ministan sufuri, Ebenezer Babatope, ya ce ba zai goyi bayan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu ba a zaben 2023.

Babatope, yayin da ya ke magana a wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin, 5 ga watan Satumba ya ce duk da shi Tinubu daga kabila daya (yarbawa) suka fito, ba jam'iyyarsyu daya ba, Daily Independent ta rahoto.

Kara karanta wannan

Wike: Babu Wanda Zai Iya Siya Na, Bana Kwadayin Mukamin Gwamnati

Tinubu da Atiku.
"Na San Tinubu Sama Da Shekaru 50, Amma Ba Zan Iya Goyon Bayansa Ba", Tsohon Minista Mai Goyon Bayan Atiku.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me yasa Babatope ba ya goyon bayan Tinubu

Tsohon ministan ya ce shi da Tinubu sun san juna fiye da shekaru 50 amma tunda ba jam'iyyarsu daya ba, ba zai iya goyon bayan tsohon gwamnan na Jihar Legas ba.

Ya yi watsi da batun mara wa Tinubu baya saboda kabilarsu daya. Tsohon ministan ya ce wannan batun na kabilanci ba zai yi tasiri ba.

Ya bayyana cewa shi mamba ne na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), kuma dan takararsa shine Atiku Abubakar, wanda ya yi imanin shine zai ci zaben shekara mai zuwa.

Babatope ya yi watsi da batun goyon bayan Tinubu saboda kabilarsu daya

Tsohon ministan ya ce:

"Ba jam'iyyan mu daya ba, duk da cewa dukkan mu yarbawa ne. Na san Tinubu fiye da shekaru 50 amma ba zan iya goyon bayansa ba tunda ba jam'iyyar mu daya ba.

Kara karanta wannan

Ni ba matsiyaci bane: Dan takarar shugaban kasan Najeriya ya ce ya fi shugaban Amurka kudi

"Shi yana APC ne, amma ni dan PDP ne."
"Babu maganar cewa yarbawa ne. Ni dan PDP ne kuma dan takarar mu, Atiku Abubakar shi zai yi nasara da izinin Allah."

Atiku: Tikitin Musulmi Da Musulmi Yasa Ban Amince Da Tinubu Ba Lokacin Da Yake Son Zama Abokin Takara Na

A wani rahoton, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce kauracewa tikitin musulmi da musulmi yasa ya ki yarda Asiwaju Bola Tinubu ya yi masa mataimaki a zaben shekarar 2007, The Cable ta rahoto.

Atiku, wanda ya yi wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo mataki daga 1999 zuwa 2007, ne ya bayyana haka yayin wata hira da aka yi da shi a ARISE TV a ranar Juma'a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel