Rikicin PDP: Atiku Abubakar Da Gwamna Wike Sun Cimma Wata Muhimmiyar Matsaya

Rikicin PDP: Atiku Abubakar Da Gwamna Wike Sun Cimma Wata Muhimmiyar Matsaya

  • Za'a sake zaman sulhu don kawo karshen rikicin dake tsakanin Atiku Abubakar da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike
  • Bayanai sun nuna cewa tuni jiga-jigan biyu suka zaɓi ranar da zasu zauna tattauna wa Ido da Ido gabanin fara kamfe
  • Ƙusoshin babbar jam'iyyar hamayya PDP, Atiku da Wike, ba su ga maciji da juna tsawon lokaci kuma alamu sun nuna su kaɗai zasu iya kawo karshen lamarin

Abuja - Wasu majiyoyi daga cikin jam'iyyar PDP sun bayyana cewa Alhaji Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban kasa, ya cimma matsaya da gwamna Wike na Ribas na sake zama a ranar Laraba 7 ga watan Satumba, 2022.

A ruwayar jaridar Independent, jiga-jigan siyasar biyu zasu gana ne domin sake karfafa zaman da suka yi a Landan makonni ƙalilan da suka shuɗe.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Fallasa Wanda Wike da Wasu Gwamnoni Suka Amince Ya Gaji Buhari a 2023

Gwamna Wike da Atiku Abubakar.
Rikicin PDP: Atiku Abubakar Da Gwamna Wike Sun Cimma Wata Muhimmiyar Matsaya Hoto: Atiku Abubakar
Asali: UGC

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ganawar Atiku da Wike a birnin Landan bai haifar da ɗa mai ido ba domin mutanen biyu sun gaza tsayuwa a inuwa ɗaya, wanda hakan ya kara tsananta rikicin.

Wata majiya tace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Abinda zan iya faɗa muku shi ne an tattake wuri cewa Waziri zai sake neman Wike cikin mako biyu bayan ganawarsu ta Landan, ina tsammanin mako mai zuwa zasu zauna, mai yuwuwa ranar Laraba idan ban manta ba."
"PDP ta fahimci inda matsalar take kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa haifaffen jihar Adamawa yana fatan kawo ƙarshen matsalar a cikin gida."

Atiku a shirye yake a yi sulhu - Majiya

Majiyar ta ƙara da cewa kofar ɗan takarar kujera lamba ɗaya a buɗe take na a zo a zauna domin lalubo hanyar zaman lafiya da haɗin kai gabanin babban zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

2023: Bola Tinubu Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Raɗa Wa PDP Sabon Suna

Haka nan, majiyar tace Atiku a shirye yake ya biya bukatun gwamna Wike matuƙar basu wuce gona da iri ba.

Wata majiyar ta daban, wacce ta yi tsokaci kan masu kiran shugaban PDP na ƙasa ya yi murabus, ya ce suna da wata boyayyar manufa.

"Duk da bana son tsoma kaina cikin lamarin amma ina son na yi tambaya, meke ingiza masu kira shugaban jam'iyya na ƙasa, Dr. Iyorchia Ayu, ya sauka a dai-dai lokacin da ya rage makonni a fara kamfe?"
"Na yarda suna da hujjar haka amma abinda ya fi damu na shi ne lokaci. Ina tunanin ya kamata mu bari sai bayan zaɓe."

A wani labarin kuma Bola Tinubu Ya Magantu Kan Rikicin Atiku da Wike, Ya Raɗa Wa PDP Sabon Suna

Tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, yace yana mamakin yadda a kai har yanzun PDP ke raye bayan ta kashe ƙasa

Kara karanta wannan

Rikici Ya Tsananta: Butulci da Girman Kai Ba Zasu Kaika Ko Ina Ba, Wike Ya Caccaki Shugaban PDP

Ɗan takarar shugaban kasa ya bayyana cewa APC ta shirya tsaf domin magance duk wasu kalubale da suka kewaye Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262