2023: Peter Obi Zai Rasa Takarsa Na Shugaban Kasa A Labour Party? Sabbin Bayanai Sun Fito Fili

2023: Peter Obi Zai Rasa Takarsa Na Shugaban Kasa A Labour Party? Sabbin Bayanai Sun Fito Fili

  • Wani sabon rahoto da ya fito ya nuna cewa akwai yiwuwar a kwace tikitin takarar shugabancin kasa na Labour Party daga hannun Peter Obi
  • Shugaban bangare guda na jam'iyyar ta Labour Party a Legas, Mista Ifagbemi Awamaridi ne ya sanar da hakan
  • Amma, shugabannin jam'iyyar na kasa sun fada wa mambobi da magoya bayansu su kwantar da hankulansu tare da cewa lamarin ba gaskiya bane

Tikitin takarar shugaban kasa na Peter Obi a jam'iyyar Labour Party a halin yanzu yana fuskantar barazana bayan rikici da ke faruwa a jam'iyyar a Legas.

Wani rahoto na jaridar Punch ta tabbatar da rikicin da ke faruwa kan jagorancin jam'iyyar a Legas kuma hakan na iya shafar sahihancin dan takarar shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Babban Jam'iyya A Najeriya Ta Dakatar Da Dan Takarar Shugaban Kasarta

Peter Obi
2023: Peter Obi Zai Rasa Takarsa Na Shugaban Kasa A Labour Party? Sabbin Bayanai Sun Fito Fili. Hoto: Peter Obi
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit.ng ta tattaro cewa wanda ya ke ganin an masa ba daidai ba a rikicin shine shugaban jam'iyyar na tsagi guda a Legas kuma dan takarar gwamna, Mista Ifagbemi Awamaridi.

Awamaridi ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 2 ga watan Satumba yayin da ya ke cewa jam'iyyar bata bi tanadin kundin tsarin dokarta ba kuma ya shigar da kara kotu.

Ya kuma yi ikirarin cewa shine halastaccen dan takarar gwamna na jam'iyyar don sunansa na jerin sunayen yan takara da ke hannun hukumar zabe INEC.

Awamaridi ya ce:

"Akwai dan takarar gwamna na jam'iyya da INEC ta futar, kuma dan takarar bai janye ba, kuma bai mutu ba.
"Idan wani ya ce zai shirya zaben fidda gwani na biyu, wannan mai barkwanci ne. An rufe wa wasu (shugabannin jam'iyyar na kasa) ido da kudi don abin da suke yi hankali ba zai dauka ba."

Kara karanta wannan

PDP: Yadda Shettima Yayi Zagon Kasa ga Kokarin Jonathan na Ceto 'Yan matan Chibok

A kan zama halastacen dan takarar gwamna na jam'iyyar, Mista Awamaridi ya ce idan aka yi la'akari da dokokin jam'iyyar, har yanzu shine halastaccen dan takara.

Ya ce:

"Takardar da suka gabatar na cewa sun nada Kayode Salako an fitar da shi a kafafen watsa labarai ne a ranar 23 ga watan Yuli, amma aka sauya kwanan wata zuwa 18 ga watan Mayu don makirci.
"Wannan takardar ba za a amince da ita ba. Tunda farko, shi (Salako) ba dan jam'iyyar LP bane. Dan jam'iyyar APC ne."

Ya ce idan za a bi takardar da aka gabatarwa Salako a matsayin ciyaman, "hakan na nufin Peter Obi ba shine dan takarar shugaban kasa na LP ba. Hakan na nufin a ranar 18 ga watan Mayu, Kayode Salako na ciyaman na LP.

"Ni, a matsayi na na ciyaman na LP, Jihar Legas, na jagoranci daligets da suka zabi Peter Obi a matsayin dan takarar shugaban kasa a ranar 30 ga watan Mayun 2022 (babban taro).

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Karamin Yaro Ne: Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, Ya yi Raddi

"Idan yanzu kana cewa daligets din da suka tafi babban taron daga Legas ba halastattu bane kuma kuri'unsu ba su da inganci, hakan na nufin taron baki daya ba halastacce bane."

Labour Party ta yi martani kan rikicin da cancantar Obi

Da ya ke martani kan cigaban, sakataren jam'iyyar na aksa Abayomi Arabambi ya bayyana cewa jam'iyyar a matakin kasa ba ta san da wannan ikirarin ba.

Amma, ya ce Mista Awamaridi ba dan jam'iyyar bane bayan ya saba wasu dokokinta.

Arabambi ya bayyana cewa Mista Awamaridi bai biya kudin jam'iyya ba kuma ya ki hallartar wasu tarruka na jam'iyya.

A kan barazanar soke takarar Peter Obi, Arabambi ya ce babu wannan maganar, kuma za a maye gurbin sunan Mista Awamaridi da ke wurin INEC da Gbadebo-Rhods Vivour a matsayin dan takarar gwamna a ranar 4 ga watan Oktoba.

Ya ce:

"INEC ta sanar da cewa ranar 4 ga watan Oktoba ne za ta fitar da sunayen yan takara da aka canja su.

Kara karanta wannan

'APC Ya Ke Yi Wa Aiki': Mambobin NNPP A Kaduna Sun Bukaci A Kwace Takarar Gwamna Daga Hannun Hunkuyi

"Kawai don sunansa har yanzu na nan baya nufin halasci. Kawai dai saboda jadawalin INEC ne."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164