Kaduna 2023: Sanata Hukunyi Na NNPP Ya Zabi Abokin Takararsa

Kaduna 2023: Sanata Hukunyi Na NNPP Ya Zabi Abokin Takararsa

  • Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP a Kaduna ya gabatar da abokin takararsa
  • Hukunyi ya zabi Dakta Sani Mazawaje daga karamar hukumar Kachia (kudancin jihar Kaduna) a matsayin abokin takararsa
  • Dakta Mazawaje ya yi godiya ga Hunkuyi bisa zabensa da ya yi, ya kuma yi alkawarin zai zama mai biyayya gare shi a yayin da za su yi aiki don kawo canji a jihar

Kaduna - Dan takarar gwamna na jam'iyyar NNPP a babban zaben 2023 na jihar Kaduna, Sanata Suleiman Othman Hunkuyi, ya gabatar da Dr Sani Mazawaje a matsayin abokin takararsa, Daily Trust ta rahoto.

Da ya ke magana wurin taron a ranar Juma'a, Sanata Hunkuyi ya bayyana abokin takararsa wanda ya fito daga karamar hukumar Kachia (Kudancin Kaduna) a matsayin mutum wanda zai bada gudunmawa sosai a cigaban demokradiyyar jihar.

Kara karanta wannan

Shekarau: Yadda Kwankwaso Yayi Min Kwantan Ɓauna, Ya ci Amanata Daga Bisani

Suleiman Hunkuyi
Kaduna 2023: Sanata Hukunyi Na NNPP Ya Zabi Abokin Takararsa. Hoto: @LeadershipNGA.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Hunkuyi ya ce:

"Na dauki lokaci na yi nazari sosai kan wadanda zan iya zaba kafin na yanke shawarar zaben Dakta Mazawaje a matsayin wanda na amince da shi kuma za mu iya aiki yadda ya kamata daga cikin sauran da suka cancanta."

Ya roki goyon bayan mutanen jihar Kaduna domin su samu damar sauya jihar daga jagoranci 'mara kyau' da ake da shi a yanzu.

Jawabin Mazawaje

A bangarensa, Dakta Mazawaje ya ce ya san dan takarar gwamnan mutum ne mai son gaskiya da adalci kuma ya bayyana shi a matsayin mai fafutikar ganin an yi adalci, The Nation ta rahoto.

"Hunkuyi wanda ya bani damar zama abokin takararsa yana da abokai a kudancin jihar fiye da arewa inda ya fito. Mutum ne mara kabilanci kuma wanda ya yi imanin cewa mutane daga bangarori biyu na jihar ne za su hadu su kawo cigaba da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Gaskiyar Abinda Ya Faru Game Da Ruwan Jifan Da Aka Yiwa Kwankwaso A Jihar Kogi

"Shi (Hunkuyi) na kowa da kowa ne bai banbancewa tsakanin mai kudi da talaka, dan siyasa ne mai hangen nesa wanda ya taimaka wurin zaben gwamnoni biyar a jihar ciki har da marigayi Ibrahim Yakowa."

Mazawaje ya yi alkawarin zai yi wa gwamnansa biyayya kuma ya fuskanci kallubalen gyara rashin adalcin da aka yi wa mutane a jihar na tsawon shekaru.

'APC Ya Ke Yi Wa Aiki': Mambobin NNPP A Kaduna Sun Bukaci A Kwace Takarar Gwamna Daga Hannun Hunkuyi

A wani rahoton, hadakar kungiyoyin matasa a jam'iyyar NNPP Jihar Kaduna sun yi kira ga shugabannin jam'iyyar na kasa su canja dan takarar gwamnan jihar, Sanata Suleiman Hunkuyi.

Kungiyar ta bayyana hakan ne cikin wani takardar korafi da ta mika wa Ben Bako, shugaban jam'iyyar NNPP na jihar, The Cable ta rahoto.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa Hunkuyi yana yi wa jam'iyyar APC ne aiki, ta kara da cewa har yanzu akwai damar a canja yan takara.

Kara karanta wannan

Gwamna Wike Karamin Yaro Ne: Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, Ya yi Raddi

Asali: Legit.ng

Online view pixel