Obasanjo: Na Yi Nadamar Goyon Bayan Buhari A 2015, Babban Kuskure Na Tafka

Obasanjo: Na Yi Nadamar Goyon Bayan Buhari A 2015, Babban Kuskure Na Tafka

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya taka muhimmin rawa wurin tabbatar Muhammadu Buhari ya zama shugaban Najeriya a 2015
  • Tsohon shugaban na Najeriya ya ce yanzu ya yi nadamar abin da ya yi kusan shekaru takwas bayan goyon bayan shugaban na Najeriya a yanzu
  • Obasanjo a baya ya nuna rashin amincewarsa da tsare-tsare daban-daban na gwamnatin Muhammadu Buhari

Twitter - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana nadamarsa kan goyon bayan shugaban kasa na yanzu, Muhammadu Buhari a 2015.

Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin hirarsa da wata marubuciya ta zamani, Ifedayo Agoro, yayin hirar da suka yi a jirgin sama.

Buhari da Obasanjo
Obasanjo Ya Ce Ya Yi Kuskure Da Ya Goyi Bayan Buhari A 2015. Hoto: @NigeriaGov.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

2023: Jonathan Na Da Ɗan Takara? Tsohon Shugaban Kasar Ya Bada Amsa

Agoro ta wallafa cikakken hirar a shafinta na Twitter, tana mai cewa ta hadu da tsohon shugaban kasar a baya-bayan nan kuma ta zauna kusa da shi a jirgin sama.

Ta ambato Obasanjon na cewa:

"Na yi babban kuskure wurin goyon bayan Buhari, bai san komai ba game da tattalin arziki. Muna tunanin zai yi yaki da rashawa da rashin tsaro, sannan ya zabi mutanen da suka san tattalin arziki da ayyuka. Babban kuskure."

Tsohon shugaban kasar kuma ya zargi matasan Najeriya da rashin hadin kai wurin yakar tsaffin yan siyasa a kasar.

Ya bayyana cewa idan matasa ba su tashi da gaske ba don canja shugabancin kasar, babu abin da zai canja.

2023: Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Dan Takarar Shugaban Kasa Da Obasanjo Ya Ke Goyon Baya

A wani rahoton daban, kun ji cewa gaskiya ta fito game da ganawar da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi da wasu yan takarar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yadda Na Magance Yajin Aikin ASUU Cikin Kwana Ɗaya, Jonathan Ya Yi Jawabi Mai Ratsa Jiki

Wani majiya da ya hallarci taron Nyesome Wike na Rivers, Seyi Makinde na Oyo, Okezie Ikpeazu na Abia da Samuel Ortom na Benue ya bayyana cewa tsohon shugaban kasar na son tabbatar da matsayinsa na uban kasa a tarihin Najeriya, This Day ta rahoto.

Tsohon shugaban kasar ya gana da gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike da bangarensa na jam'iyyar PDP, inda suka tattauna kan babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164