Tsohon Minista Ya Bayyana Halin da Lafiya 'Dan Takarar APC, Bola Tinubu, Take Ciki
- Jigon jam'iyyar APC kuma tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, yace Tinubu lafiyarsa kalau kamar kowa
- A cewar Shittu, shugabancin kasa ba daga karfin jiki bane, daga gogewa, wayewa da sauran nagartattun halaye ne
- Ya sanar da cewa, an tabbatar da cewa Tinubu baya fama da wata matsalar rashin lafiya ta bayyane ko kuma a cikin jikinsa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jigon jam'iyyar APC kuma tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu, yace 'dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ba shi da wata matsalar rashin lafiya.
Shittu wanda ya bayyana a shirin Siyasa a yau na Trust TV a ranar Alhamis, ya kara da cewa "Tinubu lafiya gare shi da kuma karfi kamar kowa."
Yace, "Bari na fada muku, lokacin da shugaban kasan yanzu bashi da lafiya, mutane da yawa sun dinga zaton zai mutu. Amma a yau ina tabbatar muku cewa garas yake fiye da ni da ku. Baya amfani da sanda kuma ba a taimaka masa wurin tafiya, haka Tinubu yake shima.
"Toh ka duba tazarar shekarun dake tsakanin Asiwaju da shugaban kasa Buhari."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jigon jam;iyyar APC din ya bayyana cewa, ba daga shekaru bane zuciyar mulkar kasar nan.
Tsohon ministan sadarwan yace shugabanci ba daga shekaru bane, akwai gogewa da sauransu.
"Ba daga shekaru bane zama shugaban kasa, ba daga iya aikin karfi bane a bayyane. Babu tantama cewa Tinubu lafiyarsa kalau kuma yana da karfi kamar kowanne mutum.
"Awkai bukatar ilimi mai kyau, gogewa, wayewa amma akwai bukatar lafiya ingantacciya kuma muna farin cikin sanar muku cewa babu wata matsala a bangaren lafiyar Asiwaju. Ina tabbata muku," yace.
2023: Da Yawa Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa Yashe Najeriya Suke da Buri, Wike
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, yace da yawa daga cikin 'yan takarar shugabancin kasa dake hararo kujerar shugaban kasa a 2023 ba su yi wa Najeriya fatan alheri saboda baitul malin kasar suke hangowa.
Kamar yadda jaridar Leadership ta rahoto, yace yana matsayin da zai fi sanin hakan kuma yace zai bayyana wadannan 'yan takarar a lokacin da ya dace ta yadda 'yan Najeriya zasu yi amfani da kuri'unsu don kayar da su.
Wike ya sanar da hakan a ranar Litinin yayin kaddamar da ayyukan titi da aka yi a Rumuesara, garin Eneka dake karamar hukumar Obi/Akpor dake jihar Ribas.
Asali: Legit.ng