Yadda ‘Yan Iskan Gari Suka Wulakanta ‘Dan takaran NNPP, Kwankwaso a Kogi
- Rabiu Musa Kwankwaso ya ziyarci jihar Kogi a ranar Laraba, ya yi nasarar bude ofishin jam’iyya da na kamfe a 2023
- ‘Dan takaran shugaban kasar na jam’iyyar NNPP ya gamu da wasu bata-gari da ake zargin su rika jifansu da ledojin ruwa
- Kwankwaso ya tuna da abokinsa tsohon gwamnan Kogi, Marigayi Abubakar Audu, ya je har kabarinsa ya yi addu’a
Kogi - Ana zargin wasu ‘yan iskan gari sun jefi tawagar Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a lokacin da ya je garin Lokoja, jihar Kogi domin yawon siyasa.
Wani rahoto da aka samu daga Punch a safiyar Alhamis ya tabbatar da cewa wasu sun rika jefawa ‘dan takaran na jam’iyyar NNPP ledojin ruwa.
Rabiu Musa Kwankwaso ya je garin Lokoja ne domin kaddamar da sakatariyar jam’iyya da kuma ofishin yakin neman zaben shugaban kasarsa.
Da isarsa wani otel da aka kama inda zai yi wa masoya da magoya bayansa jawabi, sai wadannan ‘yan iska suka duro, suka nemi su tada hayaniya.
Kamar yadda muka samu labari daga jaridar Punch dazu, a wannan otel a Lokoja ne aka rika jifar ‘dan siyasar da saran mutanensa da ledojin ruwa.
Kwankwaso ya je Ogbonicha
Kafin zuwansa babban birnin jihar Kogi, Sanata Kwankwaso ya kai ziyara zuwa garin Ogbonicha, inda nan ne mahaifar Marigayi Abubakar Audu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Kwankwaso da Abubakar Audu aminai ne a siyasa har tsohon gwamnan ya rasu a 2015. Amma magoya bayan Audu suna nan a jam’iyyar APC.
A Ogbonicha, ana zargin an samu wadanda suka bata taron magoya bayan Kwankwaso.
Hadimin ‘dan siyasar, Saifullahi Hassan ya tabbatar da cewa NNPP ta bude hedikwata a Lokoja, kuma mutane da-dama sun halarta.
Sannan kuma yace tawagar ‘dan takaran ta je kabarin Prince Audu a Ogbonicha, a karamar hukumar Ofu, inda aka yi wa marigayin addu’o’i.
An ji cewa shugaban jam’iyyar NNPP na reshen Kogi, Abdullahi Ahmadu, da wasu ‘yan takaran jam’iyyar ne suka yi wa Kwankwaso rakiya.
Siyasa ta gaji haka
Wani masoyi kuma mai ikirarin na-kusa da tsohon gwamnan na Kano, Musa Yunusa ya shaidawa manema labarai cewa siyasa ta irin wannan abin.
Musa Yunusa yace jihar Kogi tamkar gida ne a wajen Sanata Rabiu Kwankwaso.
Asali: Legit.ng