Abokin Takarar Atiku Ya Fara Tsorata, Ya Gagara Hakura da Maganar Peter Obi

Abokin Takarar Atiku Ya Fara Tsorata, Ya Gagara Hakura da Maganar Peter Obi

  • Ifeanyi Arthur Okowa ya soki amfanin da Peter Obi yake yi da coci da niyyar samun galaba a zaben shugaban kasa na 2023
  • Gwamnan na Delta yana ganin babu dalilin da Obi zai rika bi coci zuwa coci, yana tallata siyasarsa a wurin da aka sani da ibada
  • Sanata Ifeanyi Okowa shi ne ‘Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasan PDP, za su gwabza da Peter Obi a jam’iyyar LP

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kano - ‘Dan takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a PDP a 2023, Ifeanyi Arthur Okowa ya zargi Peter Obi da neman amfani da addini a siyasarsa.

Daily Trust ta rahoto Sanata Ifeanyi Arthur Okowa yana kokawa a kan yadda Peter Obi yake bin coci a kasar nan da nufin samun goyon bayan Kiristoci.

Da aka yi hira da Ifeanyi Arthur Okowa a garin Kano, ya nuna cewa bai kamata a rika jefa coci a cikin harkar siyasa ba, yana ganin hakan ba daidai ba ne.

Kara karanta wannan

Ana Rade-Radin Tinubu Yana Rigima da Shugaban APC, Jam’iyya Tayi Karin Haske

Gwamnan na jihar Delta ya yi wannan bayani ne a yayin da aka tambaye shi a game da zargin da ake yi wa PDP na hana ‘dan takararsu ya fito daga Kudu.

Gwamna Okowa yake cewa abin takaici ne wasu su fake da wannan batu, har su rika yin abin da zai iya jawowa addininsu abin magana saboda siyasa.

Daily Post ta rahoto abokin takaran Atiku Abubakar yana mai cewa ba daidai ba ne a rika kokarin amfani da coci da aka sani da yin ibada wajen cin zabe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Abokin Takarar Atiku
Ifeanyi Okowa da Atiku Abubakar Hoto: @Atiku
Asali: Twitter

Maganar Ifeanyi Okowa

“Yanzu idan aka duba abin da yake faruwa, lamarin Peter Obi kamar yana kokarin shiga coci ne, yana neman cusa kiristoci a siyasa.
Ban yarda ayi amfani da coci don cin ma manufar siyasa ba, ba wannan ne aikin da aka sansu da shi ba.

Kara karanta wannan

Rashin Sallah: Kishin Addini Ya Sa Ya Hakura da Aikin da Yake yi a Kamfanin Mai

Amma mutane suna neman abin da za su makale a kai, ko da kuwa zai taba addininsu. Ba na tunanin wannan ne abin da ya dace.”

- Gwamna Ifeanyi Arthur Okowa

Peter Obi ya samu dama

Peter Obi ya ziyarci manyan cocin da ke Najeriya a ‘yan kwanakin nan, kuma yana samun karbuwa.

A zabe mai zuwa da za ayi, tsohon gwamnan na Anambra ne kadai kirista a cikin manyan ‘yan takaran da aka tsaida, yana neman mulki a jam’iyyar LP.

Atiku zai tafi da 'yan adawa

Kuna da labari cewa yayin da ya hangi 2023, ‘Dan takaran jam’iyyar PDP Atiku Abubakar yace zai iya kafa gwamnatin hadaka da sauran ‘yan jam’iyyun adawa.

Marigayi Umaru ‘Yar’adua ya yi irin wannan a lokacin da ya nada Ministocinsa a 2007, ya yi wa jam’iyyun ANPP da PPA tayin su yi aiki tare a cikin Gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

2023: Da Yawa Cikin 'Yan Takarar Shugabancin Kasa Yashe Najeriya Suke da Buri, Wike

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng